Kungiyar Arewa ta Nemi da a Hukunta Tubabbun ‘Yan Boko Haram

 

Kungiyar Arewa ta ce sama bata yarda a saki yan Boko Haram da suka mika wuya ba.

A makon da ya gabata, kimanin yan Boko Haram 1500 sun ajiye makamansu.

Gwamnatin Borno tace ita dai yanzu tana cikin tsaka mai wuya kan yadda zatayi da tubabbun yan ta’adda,

Kaduna – Kungiyar Arewa Consultative Forum, ta yi watsi da maganar yafewa yan ta’addan Boko Haram da suke mika wuya ga gwamnati da kuma sakinsu.

Shugaban kungiyar na kasa, Cif Audu Ogbeh, ya ce wajibi ne a hukunta yan ta’addan kan laifukan da suka aikata kan yan Najeriya.

Ogbeh, wanda tsohon Ministan noma ne, ya bayyana hakan a jawabin da ya rattafa hannu kuma kakakin kungiyar, Emmanuel Yawe, ya sake a Kaduna ranar Talata, rahoton ThePunch.

Yace:

“Muna ganin yadda yan ta’addan Boko Haram ke mka wuya da yawansu. cikinsu akwai masu hada bama-bamai, kwamandoji, masu fyade, da masu satan yara.”

“Saboda haka me zamuyi da su? Kawai mu sake su kuma mu yarda da su? Gaskiya da kamar wuya.”

Kungiyar tace idan har za’a saki wadannan mutan to a saki dukkan mutanen da aka tsare a gudan yari a fadin Najeriya gaba daya.

Yace:

“Muna taya gwamnan Borno, Shehun Borno, Sanata Ndume, da daukacin yan Najeriya wajen nazari kan wannan lamari kuma shawararmu itace: A hukuntasu ko kuma a saki dukkan wadanda ke tsare a fadin tarayya.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here