Mutum 1 ya Rasa Ransa Sanadiyyar Musayar Wuta Tsakanin ‘Yan Bindiga da Sojojin Nijar a Jahar Katsina

 

Wasu ‘yan bindiga da sojojin kasar Nijar suna musayar wuta a bodar Jibiya, jahar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa yan ta’addan ne suka kai hari kauyukan dake kusa a Nijar, suka sato dabbobi.

Dan majalisa mai wakilar Jibiya, Mustapha Yusuf, yace sojojin sun biyo yan bindigan ne domin kwato dabbobin.

Katsina- Yanzun haka sojojin Nijar da wasu gungun yan bindiga suna musayar wuta a bodar karamar hukumar Jibiya, jahar Katsina.

Premium Times ta ruwaito daga majiya da dama cewa yan bindigan sun kashe soja ɗaya, sun kwace motar yakin sojojin kasar Nijar a gumurzun da aka fara tun ranar Litinin.

Dan majalisa mai wakiltar Jibiya a majalisar dokokin Katsina, Mustapha Yusuf, ya bayyana cewa yan bindigan ne suka fara kutsawa kasar Nijar, inda suka sato dabbobi zuwa Najeriya.

Meya kawo sojojin Nijar cikin Najeriya?

Honorabul Yusuf yace:

“Sojojin jamhuriyar Nijar sun shigo Najeriya domin kuɓutar da wasu dabbobi biyo bayan harin da wasu yan bindiga suka kai kauyukan ƙasar.”

“Ɗoka ta basu damar shigowa Najeriya har tsawon kilomita 30 matukar dalilin ya shafi tsaro.”

Yusuf yace yan bindigan sun kashe sojan Nijar ɗaya sannan sun kwace motar yaki guda ɗaya bayan sun musu wani kwantan ɓauna.

Ya kara da cewa wasu sojojin jamhuriyar Nijar da dama tare da wani jagoran yan bijilanti sun bata tun ranar Litinin.

Wane hali mazauna yankin suke ciki?

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa sun ga motoci aƙalla 17 cike da sojojin Nijar sun nufi wani daji.

Jim kaɗan bayan wucewar sojin sai aka fara jiyo karar harbe-hare wanda ake tsammanin sojojin ne suka buɗe wuta kan yan bindiga a dajin.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jahar Katsina, Gambo Isa, ya ƙi daga kiran wayar da ake ta masa domin jin ta bakinsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here