Mun Yafe wa Dukkan Mutanen da Suka Yake mu – Taliban

 

Kungiyar Taliban ta bayyana afuwarta ga dukkan wadanda suka yake ta a shekarun baya.

Ta ce, ba ta son gaba da kowa a yanzu, kuma ba yake-yake ne ta sanya a gabanta a yanzu.

Ta kuma cewa, burinta shi ne samar da zaman lafiya ga kasar, kuma tana shirin cimma hakan.

Afghanistan – Kungiyar Taliban ta bayyana cewa za ta tabbatar kowanne dan kasar Afghanistan ya samu damar walwala tana mai cewa ba ta bukatar abokan gaba.

A taron manema labarai da ta gudanar, mai magana da yawun kungiyar Zabihullah Mujahid, wanda ya bayyana a gaban ‘yan jarida a karon farko tun bayan da suka kwace iko, ya ce sun ‘yantar da kasar.

A cewarsa in ji rahoton BBC:

“Wannan lokaci ne na alfahari.”

“Muna son tabbatar da ganin Afghanistan ba ta sake tsunduma cikin yaki ba. Mun yafe wa dukkan mutanen da suka yake mu. Gaba ta zo karshe.”

Meye Taliban ta sa a gaba?

A rahoton Sky News, Zabihullah ya kara da cewa babban abin da Taliban ta sa a gaba shi ne samar da “doka da oda” ga babban birnin Kabul – kuma ya tabbatar wa mutanen birnin cewa za su “zauna lafiya”.

Hakanan ya ba da tabbaci kan amincin wadanda suka yi aiki tare da sojojin Amurka da na kawance.

Ya ce ‘yan Taliban “ba sa son su bar kasar” amma yana son su yi amfani da kwarewar su don yiwa sabuwar gwamnatin aiki – kuma “za a yi musu afuwa”.

Taliban “ba sa son wasu abokan gaba na ciki ko na waje”, in ji shi, sannan kuma ya ce “za mu yi aiki tare da” duniya don kirkirar hanyoyin nasara ga Afghanistan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here