Wata Ƙungiyar Dattijan Arewa Sun Nuna Fushin Su ga Shugaba Buhari
Ƙungiyar Dattijan Arewa (NEF) ta nuna damuwarta bisa matsalar tsaro da take addabar yankin arewacin ƙasar Najeriya.
A cewar Ƙungiyar, ba ta gamsu da tafiyar kunkuru da aikin babban titin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
Kazalika, Ƙungiyar tuntuba ta arewa (ACF) ta aika sakon fushin mutanen arewa zuwa ga Buhari, kamar yadda TheCable ta rawaito Emmanuel Yawe na fadi.
Ƙungiyar Dattijan Arewa (NEF) ta ce gwamnati Shugaba Muhammad Buhari ta gaza yin kataɓus don kawo ƙarshen matsalar tsaron arewacin Najeriya.
A cewar jaridar The Guardian, ƙungiyar a wani jawabi da ta fitar ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba, ta zargi gwamnatin Buhari da yin burus tare da nuna halin ko in kula ga al-ummar yankin Arewa.
Read Also:
Kakakin ƙungiyar Dattijan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya zargi gwamnatin Buhari da yin tafiyar kunkuru wajen aikin babban titin da ya haɗa jihohin Abuja, Kaduna da Kano.
Baba-Ahmed a kwana kwanan nan ya gano cewa aikin zai ɗauki tsawon shekaru biyar kafin a kammala shi.
Kungiyar Dattijan Arewa tace akwai alamar tambaya,me yasa tun shekarar 2017 aka bada kwangilar titin amma ba’a fara aikin ba sai a shekarar 2018.
Tace tafiyar kunkurun da aikin babbar hanyar ke yi hujja ce ƙarara a fili dake nuni da cewa Shugaba Buhari bai damu da matsalolin da ke addabar yankin Arewa ba kwata kwata.
Ƙungiyar tace; “babban abin da ya damu shugaban ƙasa shine kuri’ar mu”.
Wannan gwamnatin ta sake yankewa ƴan arewa hukuncin zama cikin halin ɗar-ɗar da barazana ga rayukansu tare da tattalin arziƙin yankin.