Arewa Tayi Rashin Likitan Dabbobi na Farko
Inna lillahi w ainna ilaihi raji’un.
Arewacin Najeriya ta yi rashin wani babban farfesa cikin farfesoshinta na farko a tariti.
Mai Martaba Etsu Nupe ya yi alhinin mutuwar Farfesa Shehu Jibrin Farfesan likitancin dabbobi na farko da ya fito daga Arewacin Najeriya kuma tsohon shugaban karamar hukumar Bida a jihar Neja, Shehu Jibrin, ya rigamu gidan gaskiya.
Read Also:
Jibrin wanda shine Marafan Nupe kuma Farfesa na farko da ya fito daga kabilar Nupawa ya rasu ne da safiyar Alhamis a Bida yana mai shekaru 86 bayan gajeruwar rashin lafiya.
Etsu Nupe kuma shugaban sarakunan gargajiyan jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, ya siffancin mutuwar Farfesa Shehu Bida matsayin babban rashi ga al’ummar Nupe, jihar Neja da kuma Najeriya gaba daya.
A cewarsa, marigayin babban malamin Boko ne kuma zakakurin dan siyasa, Daily Trust ta ruwaito.
“Ya kasance Uba mai soyayyar ‘yayanda a zuciya. Ya kasance mai tabbatar da zaman lafiya,” cewar Etsu Nupe.