Arewa Tana da Hanyar Mayar da Kai Shugaban je ka na yi ka – Fasto Bakare

 

Wani babban malamin coci a Najeriya wanda kuma ya taba yin takarar mataimakin shugaban kasa ga Buhari,Fasto Tunde Bakare, ya ce duk wani mai son ya mulki Najeriya sai ya yi yarjejeniya da yankin arewacin kasar.

Fasto Bakare wanda ya shaida wa jaridar Thisday hakan ya ce “arewa tana da hanyar mayar da kai shugaban je ka na yi ka.”

Faston ya ce za a iya sauya hakan ne kawai ta hanyar sauya kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bayyana a matsayin “shaidar mutuwa.”

A cewarsa, “tsarin da kundin mulkinmu yake kai a yanzu, ko ma waye zai mulki kasar, to sai ya yi yarjejeniya da arewa kuma ita arewar nan tana da hanyar dora ka a mulkin amma ba za ka zama raumi da akala ne.

“Na kan ce kusan duk abubuwan da arewa ke da su a lokacin su Ahmadu Bello a yanzu babu su. Duk masana’antun da ake da su da yanzu babu. Babu dalar gyada da saurans su.

“Abin da kawai suke da shi yanzu shi ne mulki. Suna da karfin iko,” in ji shi.

Tunde Bakare ya ƙara da cewa “Najeriya ƙasa ce da babu bangaren da zai iya cin zabe a kan kansa. Dan kudu ba zai iya cin zabe ba tare da neman arewa ba haka ma dan arewan.”

Sannan ya ce abubuwa sun taɓarɓare duk da alkawuran da wannan gwamnatin kafin ta hau mulki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here