Wata Kungiyar Arewa na Kokarin Kaddamar da Shugaban Kasa#2023
An fara tsere kan wanda zai gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar.
Wata kungiyar Arewa ta kaddamar da neman sahihin dan takara da zai zama shugaban kasa a 2023.
Kungiyar ta kuma bude idonta a kan talauci da rashin tsaro da ke yi wa yankin arewacin Najeriya barazana.
Yayinda aka mayar da hankali kan tattauna batun wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari, wata kungiya ta kafa kwamiti domin fara neman sabon shugaban kasa.
Kungiyar arewa, Progressives Movement for Democracy (PDM), ta bayyana hakan a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba, cewa an ba kwamitin damar samo sahihin dan takara wanda arewa ke gabansa, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Read Also:
Da yake magana a yayin rantsar da kwamitin, shugaban kungiyar, Muhammad Auwal Musa, ya ce arewa ta gaji da zama cibiyar talauci da rashin tsaro a kasar.
A cewarsa, manufar kungiyar shine hada kan yan arewa domin ci gaban yankin.
“Muna son hadin kai domin neman muradin arewa gabannin zabukan 2023, kamar yadda muka yi a 2014 lokacin da aka kafa APC.
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar kujerar a matsayin shugaba a 2023.
Mun yanke shawarar hada kai da kuma hada yan arewa a karkashin inuwa guda domin mu kawo ci gabanmu hadewarmu a siyasa.
“Dole sai mun yi aiki da nusar da dukkanin jam’iyyun siyasa su gano sahihan yan takara wadanda za su iya wakiltan mutane a dukkan matakai.
An tattaro cewa mambobin kwamitin na a fadin jihohin arewa maso yamma.”