Mutan Arewa Mazauna Legas Sun Bayyana Niyyar Baiwa Tinubu Kuri’u Miliyan 1.5
Jama’ar Arewa mazauna Legas sun bayyana niyyar tarawa Tinubu kuri’u miliyan 1.5 a zaben 2023.
Yan Arewan sun ce ba zasu kasa a gwiwa ba wajen baiwa Bola Ahmed Tinubu kuri’un da suka wuce wanda suka ba Fashola.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC.
Jihar Legas – Mutan Arewa mazauna jihar Legas sun bayyana niyyar baiwa Asiwaju Bola Tinubu kuri’u miliyan 1.5 a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa, rahoton The Nation
Wannan ya bayyana ne yayin wani taron kaddamar da Alhaji Sa’adu Gulma, matsayin shugaban jam’iyyar APC na al’ummar Arewa dake tashar Tirela na Oko-Oba Abattoir.
Read Also:
Sa’adu ya ce zabensa matsayin shugaban al’ummmar Arewa na jihar Legas zai bude kofar alheri ga yan Arewa a jihar sosai.
Ya ce kudirinsa shine tabbatar da al’ummar Arewa sun samarwa Tinubu kuri’u miliyan 1.5 a zabe mai zuwa.
Shugabar mata Hajia Fatima Bako, ta jaddada amfanin mata shiga fagen siyasa, inda ta ce lokaci ya yi da za a biya Asiwaju da kuri’u bisa irin alheran da ya yake yiwa mutane ba tare da la’akari daga inda suka fito ba musamman bambancin addini ko yare kamar yadda Sunrise News ta rawaito.
Wata tsohuwar shugabar mata Hajiya Azabe ta tabbatar da cewa yan Arewa za su ba da kuri’u domin tabbatar da Asiwaju ya lashe zaben.
Al’umomin Arewa da suka halarci taron sun hada da mutanen jihohin Sokoto, Kebbi, kungiyar dilolin shanu, kungiyar cigaban Kabilar Shuwa Arab, da kungiyar yan Okada na yankin Arewa da sauransu.