Anyi Asarar Rayukan Mutane 20 da Kuma N5.6m Sakamakon Gobara a Jahar Kano
Hukumar kwana-kwanan jahar Kano ta ce mutane 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon gobara a jahar a watan Augusta.
A cewar hukumar, an yi asarar dukiyoyi wadanda za su kai naira miliyan 5.6 duk a cikin watan da ya gabata.
A ranar Laraba, jami’in hulda da jama’an hukumar, Saminu Abdullahi, ya bayyana hakan a wata takardar kiyasi.
Kano – Hukumar kwana-kwanan jahar Kano ta ce an yi asarar rayukan mutane 20 da kuma dukiya mai kimar naira miliyan 5.6 sakamakon gobarar da aka yi a wurare daban-daban a fadin jahar cikin watan Augusta.
Daily Nigerian ta rawaito cewa, Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’an hukumar ne ya bayar da wannan kiyasin a wata takarda a ranar Laraba a jahar Kano.
Read Also:
A cewar Abdullahi, hukumar ta samu nasarar ceton rayuka 102 da dukiyoyi da suka kai kimanin naira miliyan 14.7 sakamakon gobara 16 da ta auku a fadin jahar a cikin watan Augustan wannan shekarar.
A cewarsa, hukumar ta amsa kiran gaggawa daga gidajen hukumar guda 27 da ke fadin jahar a cikin wannan lokacin, Daily Nigerian ta wallafa.
“Hukumar ta je wurare 81 bayan kiran ceton rai da aka yi mata da kuma kira 14 wadanda ba gaskiya bane daga mutanen jahar,” a cewarsa.
Abdullahi ya alakanta mafi yawan gobarar da rashin kulawa wurin amfani da wutar gas wurin girki da kuma gobara sakamakon wutar lantarki.
Ya shawarci mazauna yankin da su dinga kulawa don gudun barkewar gobara.
Ya kara da shawartar iyaye akan su tabbatar sun dakatar da yaransu daga yin iyo a rafuna a halin yanzu kuma su kula da inda zasu dinga zuwa.