Dr. Kabir Asgar Zai Wallafa Littafin Tarihin Marigayi Sheikh Albani Zaria

 

Kabir Abubakar Aminu ya na rubuta littafin da ya tattara rayuwar Sheikh Muhammad Auwal Adam.

A matsayinsa na tsohon dalibi, malamin ya san wanene Albaniy Zaria da irin hidimarsa ga aikin addini.

Malam Muhammad Auwal Adam Albaniy Zaria ya na cikin manyan malaman addini da aka amfana da su.

Kaduna – Kabir Abubakar Aminu, malamin addinin Musulunci ne a garin Zariya, jihar Kaduna wanda almajirai su ka fi sani da Asgar.

Wannan malami ya bayyana cewa ya na shirin karkare aikin littafi na musamman da ya rubuta kan tarihin Sheikh Muhammad Auwal Adam.

Littafin dalibin babban malamin zai yi bayani game da rayuwa da harkar malantar Auwal Adam wanda ya fi shahara da Albanin Zariya.

Dr. Kabir Asgar zai wallafa tarihin Albani

Tare da yin addu’a ga malamin na sa, Dr. Kabir Asgar ya ce abin da ya rage shi ne malaman harshe su duba littafin da aka wallafa da Hausa.

TARIHIN RAYUWA DA KARANTARWAR MALAM ALBANI ZARIA (Allah Ubangiji Ya Gafarta Masa)

AlhmdullLah. Kusan na kammala wannan aikin wanda na ɗauki shekaru ina yi.

A yanzu haka wani masanin Harshen Hausa ya duba mani kura-kurai. – Kabir Asgar

Marubucin ya dace da wannan aiki

Wani abokinsa a harkar karantarwa, Muhammad Abdulqadir Sheethu ya ce Dr, Kabir Asgar ɗaya ne daga cikin manyan almajiran marigayin.

Baya ga cibiyar marigayi Albani, marubucin ya na koyar da ilmin larabci a jami’ar ABU Zariya, ya dauki shekaru ya na tattaro tarihin shehin.

Abu Shiithu ya kara da cewa Asgar masanin tarihi ne da ilimin tantance labari, kuma kwararre a kan harsunan Larabci, Ingilishi da kuma Hausa.

A cewarsa wanda ya hada waɗannan siffofi uku, ya cancanta da rubuta tarihin malami irin Albaniy Zaria wanda aka kashe a farkon 2014.

Malam Asgar da Albany

Da yake bayani game da dangantakarsa da bijimin malamin, Kabir Asgar a shekarun baya ya kamanta Albani Zariya da matsayin uba.

“Shi Mal. Albani Zaria (رحمه الله) a wajena malami ne kuma uba. Mutum ne mai zurfin hangen nesa. Ga shi da son alheri. Ga tarin karatu na ɗar-ma-sa’a. Ba shi da manufa sai ƴaɗa sunnar Manzon Allah (SAW). Mutum ne mai kwarjini sosai. In ba ka san shi kai tsaye ba, zai yi wuya ka fahimce shi da wuri. Musamman in ka fara gamuwa da magautansa. Amma in ka sa san shi kai tsaye, to ka san irin sauƙin mu’amalarsa da falsafarsa game da rayuwa da tawali’unsa da kuma tarin manufofi na nesa kamar bature.

Mal. Albani zai koya ma karatu, ya ba ka kudi ya ba ka shawara akan ilimi da kasuwanci da noma da aure da sauransu.”

– Kabir Asgar

A dalilin haka Legit.ng Hausa ta tuntubi Malam Ibrahim El-Caleel wanda dalibin ilmi ne a Zariya, shi kuma ya yaba da yunkurin malamin na sa.

El-Caleel ya nuna muhimmancin duniya ta san tarihin malamai irinsu Sheikh Albani Zariya wanda su ka yi rawar gani wajen gyara al’umma.

“Hakika wannan littafin da malaminmu Dr Kabir Abubakar Aminu (Asgar) ya wallafa, muhimmin aiki ne.

Dalili shine:

Shaikh Muhammad Auwal Albaniy Zaria yana daga cikin fitattun malamai a kasar Hausa wadanda suka yi amfani da ilimi wajen samar da juyin yanayi a wannan karni na 21 Miladiyyah.

Shaikh Albaniy Zaria da kansa cikin harshen turanci ya kan ce, “knowledge in youth is wisdom in age”.

Ma’ana wai, “tarbiyyar matasa cikin ilimi shine yake kawo habakar hikima a yayin da shekaru suka cim musu”.

Don haka tarihin muhimmin malami irin wannan abune da ya kamata a killace shi, domin matasan yau da na gobe su ga kyakkyawar misali na irin gwarazan malamai wadanda suka yi aiki tukuru wajen gina al’ummah.”

– Ibrahim El-Caleel.

Fatawar Kabir Asgar a kan sallar idi

Kwanakin baya kun ji malamai sun ce bai dace mutum ya ki yin sallar idi ba tare da kwakkwaran dalili ba, ana so kowa ya fita zuwa ibada a ranar sallah.

Kamar yadda Dr. Kabir Asgar ya bayyana, babu laifi mutum ya karbi aron kaya daga wajen ‘danuwansa domin ya fito acan-acan a wannan rana ta murna.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com