Daga Anas Saminu Jaen

Ina zaune a wani sashi na jihar Kano wajan wani sayar da abinci sai ga wasu samari su biyu sanye da ƙananun kaya ina zaune suka zauna a kusa da beburin da nake, na kammala cin Sinasir da miyar dage-dage ina kallon wata tsaha ana fim ga ragowar Kokakola ina kurɓa sai ka ce wani Sa’eed Usman Assalafy.

Sai na ji cikin matasan ɗayan yana bawa ɗaya labari yana cewar Na Manta Sunan da ya kira ya ce kaga duk shaye-shayen da muke yi ko, gaskiya ni ba zan iya biyan kuɗi a yi min irin Allurar nan ba mai sa silo saboda tana sa hauka kuma wai idan ta bugar da mutum ko Awa guda mutum ba zai yi cikin silo ba ta sake shi wannan yana ɗaya daga ciki abun da yasa na tsaneta wallahi, ɗayan da ake bawa labari ya ce hakane ai kaga shi yasa muka tsaya iya sai ya faɗi sunan wata ƙwaya koma irin maganin murannan ne na ruwa Ko Yama Sunan Oho! na manta, sai ya ce ta ishe mu ko kuwa ya ka ce abokina ya ce shi yasa nake son ka, ka gane yanzu kurum muna tashi daga nan mu wuce wurin Buros ko zamu samu kaya yau sama na ke son hawa.

Kwatsam sai idon ɗayan ya kawo inda nake zaune sai ya kira sunan ɗayan ya ce ga wani Ustaz mai Gemu yana jin mu, sai shi kuma ɗayan ya ce ai wannan da ganin sa CIKI NE BA WAJE BA wai a she dani suke ina jiran a kammala fim ɗin da nake kallo saboda ina son fim wanda ake ragargazar wuta sai ɗayan ya ce Ustaz ɗan Allah ba mu abun zakucen nan mana na tura masa suka zara to a nan sai na fuskanci ni ne Ustaz ɗin, bayan sun fita sai na girgiza kai na ce yau na zama ɗan kauye na ji wani sabon karatu ga masu shaye-shaye sai na yi dariya na ce lallai masu iya magana sun yi gaskiya da suke cewar Mahaukaci Ya Faɗa Riya ya ce shi wankan sa yake yi to haka wannan samarin biyu ƴan zamani sun jima suna hauka amman ba su san basa hauka ba.

Tambaya: Har na zo gida ina tunanin da nanata kalmar CIKI NE BA WAJE BA, idan akwai wanda yasan me suke nufi a ya wayar min da kai?

Babban abun da yake ƙara daure min kai shi ne da yawan matasan mu a yanzu wai idan mutum baya shaye-shaye ko baya cikin ƴan dil shi ba wayayye ba ne gaskiya sai iyaye sun tashi tsaye wurin rainon tarbiyar yara, haka al’ummar unguwanni na sha faɗar cewar mutane idan suna ganin matsala ko ta shaye-shaye da sauran su suna yin shiru wai abun bai shafe su ba to ai kuwa ya shafe ka domin matsalar kowace iri ce Gobarar Titi Ce idan ta shiga gidan maƙofcin ka idan ba a ɗauki mataki ba wataran gidanka zata faɗo musamman idan yaran naku suna mu’amulla da juna, suma mahakunta shugabanni da jami’an tsaro sai sun ji tsoron Allah cikin lamarin su, Allah ya maganta mana wannan matsalar ta shaye-shaye da ta yi tsamari a cikin al’ummar mu ma su yi Allah ya shirye su ya tsare mu ya tsare zuri’ar mu.

 

The post Ashe ‘yan shaye shaye na tsoron yin hauka? appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here