Asusun ba da Bashin Karatu na Najeriya Zai Fitar da N850m
Asusun ba da bashin kuɗin karatu a Najeriya ya ce zai fitar da naira miliyan 850 a yau Laraba ga ɗaliban da suka nemi bashin.
Read Also:
Wannan ƙari ne kan naira biliyan 1.7 da asusun na Nelfund ya riga ya bai wa ɗalibai kusan 20,000, kamar yadda shugaban asusun Akintunde Sawyer ya bayyana yayin taron manema labarai a Abuja.
Tun da farko, Mista Sawyer ya ce an amince da bayar da bashi 260,000 ciki har da kuɗin karatu da na zuwa makaranta.
Ɗalibai Najeriya kusan miliyan ɗaya da 200,000 ne ake sa ran za su amfana da wannan shiri da gwamnatin Bola Tinubu ta ƙaddamar a shekarar da ta gabata.