Yajin Aiki: Kungiyar ASUU ta Bai wa Gwamnatin Najeriya Wa’adin Mako 3

 

Kungiyar malaman jami`a a Najeriya ASUU ta bai wa gwamnatin kasar wa`adin mako uku ko ta cika alkawarin da ta yi na biyan wasu bukatun `ya`yanta ko kuma su shiga yajin aiki.

Kungiyar ta yanke shawarar bai wa gwamnati wa`adin ne a wani taron majalisar kolinta a Abuja.

Kungiyar ASUU ta bayyana cewa ta yanke shawarar bai wa gwamnati mako uku ne ko ta cika alkawarin da ta y iwa `ya`yanta yau tsawon shekara ko kuma ko kuma ta umurce su da su shiga yajin aiki na sai abin da hali ya yi, saboda sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba.

Shugaban kungiyar na kasar Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya jagoranci zaman ya ce ba su da zabi face ba da wa`adin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here