ASUU: Kungiyar ta Janye da Yajin Aiki
Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta janye daga yajin aikin da ta kwashe watanni tara tana yi.
Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai da safiyar Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020 a birnin tarayya Abuja.
Read Also:
Sanarwan ya biyo bayan ganawar kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya tun daren Talata.
Ogunyemi ya kara da cewa mambobin kungiyar ASUU sun janye yajin aikin ne da sharadin gwamnati ta cika alkawuranta.
Muddin gwamnati ta saba, a cewarsa, zasu koma yajin aiki ba tare da sanarwa ko talala ba.
Yayinda aka tambayesa shin an fara biyansu albashinsu da suke bi, ya ce an fara biyansu amma ba’a gama ba.
Ya jaddada cewa ba dan rashin albashi suka tafi yajin aiki ba.