Rabiu Kwankwaso: Shugaban Jam’iyyar APC ya Mayarwa da Tsohon Gwamnan Kano Martani

 

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya mayarwa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso martani.

A baya bayan nan, Kwankwaso ya ce baza su sake yarda a maimata musu ‘inconlusive’ ba a zaben 2023 kuma sai dai ‘a mutu, ko ayi rai’.

A martaninsa, Abbas ya ce jam’iyyar APC za ta ‘murde’ zaben na 2023 kuma babu abinda zai faru domin a cewarsa gwamnatinsu ne.

Shugaban wucin gadi na jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya mayarwa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso martani kan maganganun da ya yi game da zaben gwamna na 2023 da ke tafe.

Idan za a iya tunawa, Kwankwaso ya ce jam’iyyar PDP ba zata sake yarda a maimaita mata abinda ya faru a zaben gwamna na 2019 ba inda aka ce zaben bai kammala ba ‘inconclusive’ a yayin da dan takararta ke kan gaba da kuri’u 26,655.

Da ya ke maida martani, shugaban na APC a jihar ya bugi kirgi ya ce jam’iyyar za ta ‘murde’ zaben gwamna na 2023 kuma babu abinda zai faru, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Abbas yayin da yake yiwa ‘yan jam’iyyar jawabi yayin rantsar da kwamitin kula da jam’iyyar na APC a ranar Talata a gidan gwamnati ya kara da cewa jam’iyyar APC zata yi amfani da irin tsarin da tayi amfani da shi wurin ‘murde’ zaben mazabar Gama.

Har wa yau, Mista Abbas ya kuma shaidawa ‘yan jam’iyyar APC cewa kada su raga wa ‘yan Kwankwasiyya ko a zahiri ko gidajen rediyo inda ya ce zaben na 2023 bai za su dauke shi da wasa ba.

“Kwankwaso ya ce zaben gwamna na 2023 zai zama ‘ko a mutu, ko a yi rai’. Toh, a shirye muke. Ba ragwaye bane mu. Mun shirya wa yakin. Ba mu tsoron mutuwa.

“Ga magoya bayan mu, kada ku raga wa ‘yan Kwankwasiyya, idan sun zage ku a rediyo ko a zahiri, kada ku tausaya musu.

“Bari in fada muku, zamu murde zaben 2023 kuma babu abinda zai faru. Za mu maimaita abinda muka yi a mazabar Gama idan 2023 ta zo kuma ba abinda zai faru. Wannan lokacin mu ne. Wannan gwamnatin mu ne,” in ji Mista Abbas.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here