ASUU ta Saki Muhimmin Sako ga Dalibai, Iyaye da Malamanta
Kada ku sa ran komawarmu makarantu, nan kusa, cewar ASUU ga dalibai da iyayensu, sannan malamai su nemi wata halastacciyar hanyar samun kudi.
Shugaban kungiyar, na yankin Abuja, ya sanar da hakan a wani taro da suka yi a Abuja, inda yace gwamnati ta yi wa ASUU rikon sakainar kashi.
Sannan babban abin mamaki shine yadda ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ya fito yace an biya malamai albashi, duk da ya san ba hakan bane.
Jiya ASUU ta ce kada iyaye ko dalibai su sa ran za su dakatar da yajin aikinsu nan kusa, inda ta shawarci malaman jami’a da su yi kokarin samun wata hanyar samun na tuwo.
Shugaban kungiyar na yankin Abuja, Farfesa Theophilus Lagi, ya sanar da hakan a wani taro da suka yi a jami’ar Abuja, inda yace za a cigaba da zaman gida har sai gwamnati ta yi abinda suke so.
Ta zargi gwamnatin tarayya da nuna halin ko in kula ga harkar ilimi.
Read Also:
Kamar yadda shugaban kungiyar yace: “Yau ina so in sanar da ‘yan Najeriya, musamman dalibai da iyaye cewa, kada su sa ran ASUU za ta dakatar da yajin aikinta wanda ta fara tsawon watanni da suka gabata, saboda har yanzu gwamnati bata nuna damuwarta ba wurin samar da abubuwan da suka kamata.
“Muna shawartar ‘yan kungiyarmu da su nemi wata hanyar samun kudi na halas, saboda gwamnati ta rike mana albashi tun na watan Fabrairun 2020.”
Kungiyar ta zargi ministan kwadago da ayyuka, Dr Chris Ngige da yin talalabiya ga harkokin ilimin Najeriya, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Kungiyar ta ce Ngige ya fara shisshigi da zakewa, don har ya zama kakakin babban akawun tarayya, maimakon nemo mafita ga malamai. Ya mayar da hannun agogo baya. Ya nuna kiyayya karara ga ASUU.
“Har mamaki Ngige ya bamu, yadda ya fito gaban kowa babu kunya ba tsoron Allah, yana sanar da duniya cewa an biya malamai kudadensu, wadannan kalaman sun rage darajarsa, duk da ya san ba a biya albashin ba, tun na watanni 6 zuwa 9 da suka gabata.” yace.