Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Kasa(ASUU) ta Shiga  Ruɗu da Tsilla-Tsilla

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa, (ASUU) ta ruɗe, ta kamu da ruɗani, ta kuma afka cikin kame-kame da tsilla-tsilla akan mai shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), a saboda binciken hukumarsa ya gano cewa manhajar ƙungiyar ta tsarin biyan albashi (UTAS) ba ta da ingancin karɓa a hukumance.

A baya sun yi barazanar janye takardarsa ta shaidar kammala jami’a sun ga ba abu ne mai iyuwa ba, kuma ko ma da ace mai iyuwar ne sun tabbata hakan ba wata illa da za ta yi masa, hakan tasa su ka sake salo da kurarin wai a sauke shi daga shugabancin hukumar.

Sai dai kuma, sun manta da cewa mai girma shugaban ƙasa, Malam Muhammadu Buhari (GCFR) wanda shi ne ya naɗa shi a kan matsayin, ya yarda da shi, ya kuma gamsu matuƙa da aikin da ya ke a bisa kan matsayin.

Haka zalika, mai girma ministan sadarwa da tattalin arziƙin fasahar zamani Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), wanda shi ne ya gabatar da shi ga shugaban ƙasa, kana kuma a ƙarƙashin kulawarsa ya ke aiki ya yarda da shi, ya kuma gamsu matuƙa da yadda ya ke tafikar da aikinsa batare da matsala ba.

Baya da bayan haka, al’ummar Nageriya ma shaida ne, sun gamsu da shi matuƙa, su na kuma ganin tasirinsa a bisa kan wannan matsayi. Indai akan aikinsa ne babu wani wuri da za a kalla a ce ya gaza. Duk wanda ka ji ya kushe shi, ko ya nemi a sauke shi to sai dai akan ƙiyayya ko son zuciya kamar misalin son zuciyar ta (ASUU) ba dai gazawar aiki ko illa ba.

Saboda haka, wannan kurari na ƙungiyar (ASUU) shi da zance a teburin mai shayi duk uwa ɗai uba ɗai ne, (anan aka yi shi anan za a bar shi), Malam Kashif Inuwa zama daram-dam a hukumar (NITDA) sai dai ya bar matsayin a dalilin samun cigaba da ƙarin matsayi ba dai a sallame shi ba Bi’izinillahi Ta’ala, domin kowa ya gamsu da shi, kuma Allah Ya na tare da shi.

-Garba Tela Haɗejia
Lahadi, 17 ga watan Afrelu, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here