ASUU: Babu Wata Yarjejeniya Tsakanin mu da Gwamnatin Tarayya

Kungiyar Malaman Jami’a ta yi magana game da yajin-aikin da ta ke yi.

Shugaban ASUU ya ce gwamnati ba ta cika duka alkawuran da ta yi ba.

Biodun Ogunyemi ya karyata ikirarin da Minista ya yi na shawo kansu.

Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta ce sam ba a kai ga matakin karshe na janye dogon yajin-aikin da ake ta faman yi a jami’o’in gwamnati ba.

Jaridar Vanguard ta rahoto kungiyar ta na cin-karo da ministan kwadago, Dr. Chris Ngige, wanda ya fito ya na nuna yajin-aikin ya kusa zuwa karshe.

A cewar Chris Ngige, an biya wa ASUU shida daga cikin bukatu tara da ta gabatar wa gwamnati.

Da ya ke hira da Vanguard a ranar 15 ga watan Nuwamba, shugaban kungiyar ASUU, Biodun Ogunyemi ya ce gwamnati ba ta cika alkawuranta ba.

Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce: “A iyaka saninmu, babu abin da aka yi wa mutanenmu, kuma ba mu son alkawuran bogi.”

Shugaban ASUU na kasa ya ce: “Bari mu dauki batutuwan daya bayan daya.”

“Albashinmu da aka hana na watanni hudu zuwa takwas, su na nan har yau ba a biya ba. Da an biya, da mun ji. Haka maganar alawus din karin aikin koyarwa.”

Ba a kai ga kafa kwamitin ziyara a jami’o’i ba, idan da an yi hakan, da ‘Yan Najeriya sun ji sunayen wadanda aka zaba kamar yadda gwamnati ta sanar.”

“Ba a duba lamarin kutsen da gwamnatocin jihohi su ke yi wa jami’o’i ba. Ba a koma kan batun sake duba yarjejeniyar 2009 ba.”Inji Farfesa Biodun Ogunyemi.

Shugaban kungiyar ya kuma ce ba a fara dabbakar da yarjejeniyar 2019 ba. Bayan haka kungiyar ta zargi gwamnati da bude mata shafin bogi a dandalin Twitter.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here