Atiku ya Koka Kan Abun da ya Kira da Rashin Adalci Wajen Nada Shugabannin Hukumomin Tsaro a Najeriya

 

Atiku Abubakar ya soki abun da ya kira da rashin adalci wajen nada shugabannin tsaro a fadin Najeriya.

A ranar Laraba, 16 ga watan Nuwamba. dan takarar shugaban kasar na PDP ya yi ikirarin cewa shugabannin hukumomin tsaro 17 duk yan arewa ne.

Atiku ya ce hakan zai sauya idan ya hau karagar mulki domin zai nada yan Najeriya daga dukkan yankuna a ma’aikatar tsaro.

Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya yiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wankin babban bargo a ranar Laraba, 16 ga watan Nuwamba.

Atiku ya koka kan abun da ya kira da rashin adalci wajen nada shugabannin hukumomin tsaro a Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa a yanzu haka, shugabannin hukumomin tsaro 17 a fadin Najeriya duk sun fito ne daga yankin arewacin kasar, Channels TV ta rahoto.

Zan kawo hadin kai a Najeriya – Atiku

A yayin zantawa da mambobin kungiyar editocin Najeriya a Abuja, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce idan ya hau karagar mulki, hakan zai canja domin gwamnatinsa zata hada kan kasar ta hanyar kawo kwararru daga dukka bangarorin kasar cikin ma’aikatar tsaro.

Kalamansa:

“A yau, muna da shugabannin 17 a hukumomin tsaro daban-daban. Dukkansu sun fito ne daga arewa. Ba zan yi haka ba. Zan tabbatar da ganin cewa kowani yanki ya samu wakili a wadannan hukumomi na tsaro. Wannan ma wata hanya ce da z aka iya hada kan kasar nan sannan ka ba kowani yanki damar jin ana yi da shi.

“PDP zata kafa gwamnati na hadin kan kasa. Za mu dauko yan adawa da suka sha kaye sannan mu ci gaba daga nan. Wannan ce hanya daya da za a kawo hadin kan kasar nan kuma za mu fara tafiyar.”

Zan kara yawan yan sanda da sojoji – Atiku

Atiku ya bayyana cewa yana shirin rubanya yawan rundunar yan sandan Najeriya da na sojoji a matsayin wani yunkuri na karfafa tsaro da rage yawan marasa aiki, The Guardian ta rahoto.

Ya yi bayani:

“Da zaran ka rubanya karfin rundunar yan sandan Najeriya, watakila kana maganar kimanin 700,000 ko fiye da haka. Da wannan za ka rage yawan rashin aiki.

“Haka kuma, za mu isar da wannan aiki zuwa ga rundunar soji. A lokacin da zaka kammala hakan, za ka ga cewa ka fitar da mutum fiye da miliyan daya daga cikin marasa aikin yi.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here