Atiku Abubakar ya Magantu Kan Kashe Matafiya Musulmai a jos
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da kisan da akai wa musulmai a Jos.
Atiku ya kuma roki yan Najeriya da su bada gudummuwarsu wajen taimakawa jami’an tsaro su samu nasara.
Ya yi jimami da kuma ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayuwarsu tare da fatan samun rahamar Allah.
Adamawa – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da kisan matafiya a Jos da sauran kashe-kashen da ake a sassan Najeriya, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Read Also:
Aƙalla mutum 23 aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 23 suka jikkata a kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta arewa ranar Asabar da safe.
Atiku ya roki yan Najeriya da su baiwa jami’an tsaro haɗin kai domin su fuskanci wannan yaƙin kuma su samu nasara.
Gwamnati ta kara zage dantse
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kara zage dantse da jajircewa domin dawo da zaman lafiya a faɗin kasar nan.
A jawabin da kakakinsa, Paul Ibe, ya fitar, Alhaji Atiku yace:
“A yanayin halin da kasar mu ta shiga na rashin tsaro, jami’an tsaro na iyakar bakin kokarinsu.”
“Amma idan irin waɗannan abubuwan suna faruwa da kuma raɗaɗin dake biyo bayansa zai sa muji kamar ba ayi komai ba.”
Atiku ya mika ta’aziyyarsa ga wadanda lamarin ya shafa
Tsohon mataimakin shugaban ya yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda aka kashe tare da nuna damuwarsa kan yadda suka haɗu da ajalinsu cikin mummunar yanayi.
Ya kuma yi Addu’a tare da fatan Allah ya kawo karshen halin da Najeriya take ciki kuma ya gafartawa mutanen da aka kashe.