Atiku Abubakar ya yi Martani Kan Zargin Takardun Bogi na WAEC

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi martani kan zargin cewa ya yi jabun takardar shaidar jarrabawar kammala sakandare mai dauke da suna “Sadiq Abubakar”.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a babban zaben 2023, ya tabbatar cewa takardarsa ta kammala sakandare na dauke da sunan “Sadiq Abubakar” amma ya yi rantsuwa na kotu ya canja sunansa bayan ya ci jarrabawar.

Dele Momodu, jigo na jam’iyyar PDP, ya tabbatar da martanin na Atiku a wallafar da ya yi a kafar sada zumunta a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba.

Rubutun da ya yi a kafar X ta ce:

“Yan APC masu zumudi suna ta zargin cewa mai gida na Alhaji Atiku Abubakar (GCON) ya kirkiri takardar bogi hakan yasa na tura masa zargin kuma ga amsar da ya bada: “Eh na yi amfani da Sadiq Abubakar yayin rubuta jarrabawar WAEC kuma bayan na ci jarrabawar na yi rantsuwa a kotu na cewa ni ne dai Atiku Abubakar. Na tafi ABU a matsayin Atiku Abubakar kuma ya ci jarrabawa na a matsayin Atiku Abubakar.

“An yi min tambayoyin daukan aiki a Gwamnatin Tarayya a matsayin Atiku Abubakar kuma an dauke ni aiki a Hukumar Kwastam a matsayin Atiku Abubakar. Don haka ina kirkirar ta bogi?” – ATIKU ABUBAKAR.”

Dakaci karin bayani …

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com