Dalilin da Yasa Kotu ta Tsige Dan Takarar Gwamnan APC na Jihar Bayelsa

 

Kotun Abuja ta yanke hukunci a shari’ar takarar Timipre Sylva, a matsayin dan takarar gwamnan APC.

Yan makonni kafin zaben gwamnan jihar Bayelsa da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023, babbar kotun tarayya, ta tsige Sylva.

Hakan na zuwa ne yan makonni bayan APC a jihar Bayelsa ta tarbi tarin mambobin jam’iyyar PDP da Labour Party a inuwarta.

FCT, Abuja – Wani rahoto da ke zuwa ya bayyana cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta dakatar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Timipre Sylva, daga yin takara a zaben gwamnan jihar Bayelsa da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban.

Babbar kotun tarayyar ta yanke hukuncin ne a daren ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba.

Dalilin da yasa kotu ta tsige dan takarar gwamnan APC Jaridar ThisDay ta rahoto cewa da yake yanke hukunci, Mai shari’a Donatus Okorowo, ya riki cewa zai zama take kundin tsarin mulkin 1999 idan aka bar Sylva ya yi takara, tunda an taba rantsar da shi sau biyu kuma ya yi aiki a matsayin gwamnan jihar na shekaru biyar.

Alkalin ya kuma ayyana cewa Sylva, dan takarar na jam’iyyar APC, bai cancanci yin takara a zaben ba saboda idan ya ci zabe kuma aka rantsar da shi zai shafe fiye da shekaru takwas a karagar mulki a matsayin gwamnan jihar.

Da yake misali da lamarin Marwa da Nyako a kotun koli, Okorowo ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin kasar ya bayyana cewa kada a zabi wani mutum a matsayin gwamna fiye da sau biyu kuma cewa jam’iyyun da ke shari’ar sun yarda cewa an zabi Sylva sau biyu.

Ya ci gaba da bayyana cewa idan aka bar Sylva ya yi takara a zabe mai zuwa, hakan na nufin mutum na iya takara iya adadin da yake so.

Hakan na zuwa ne bayan APC ta yi ikirarin cewa babu baraka a cikin sansaninta gabannin zaben na jihar Bayelsa kuma cewa duk masu ruwa da tsaki a jihar suna kan tafarki daya na kawowa dan takarar jam’iyyar, Sylva nasara a zaben, rahoton Daily Trust.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com