Atiku na Son Zama Shugaban Kasa Don ya Azurta Yaransa 31 – Achimugu
Michael Achimugu ya fito ya sake yi wa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar terere gabannin babban zaben 2023.
Tsohon hadimin dan takarar na PDP ya ce Atiku na da kudirin ganin yaransa sun zamo attajirai kamar shi bayan ya mutu don haka yake son gaje Buhari.
Achimugu idan har yan Najeriya na son magana ta gaskiya toh lallai shigar Atiku Aso Rock babban kalubale ne ga kasar.
Michael Achimugu ya gargadi yan Najeriya a kan zabar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar a zabe mai zuwa, cewa shi din ba mutumin kirki bane.
Achimugu wanda ya kasance tsohon hadimin Atiku ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a wani shiri na TVC a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu, yana mai cewa shugabancin Atiku zai zamo annoba ga yan Najeriya.
Atiku na son zama shugaban kasa don ya azurta yaransa 31, Achimugu
Har ila yau, Achimugu ya ce tsohon ubangidan nasa na son zama shugaban kasar Najeriya ne saboda yara 31 da ya haifa, cewa so yake yi su zamo attajirai tamkar shi idan baya doron kasa, rahoton Sahara Reporters.
Read Also:
Ya yi ikirarin cewa kamar yadda suke yi a jihar Adamawa wajen fafutukar samun manyan mukamai, haka suke niyan yi idan har ya samu damar shiga fara shugaban kasa.
Ya ce:
“Atiku ba yaro bane. A duk sanda ya mutu, yana so yaransa su zamo attajirai kuma masu iko kamar shi. Wasu lokutan akwai misalai da dama a Najeriya, haka tara wannan arziki na ‘ya’ya, jikoki da tattaba kunne.
“Don haka kamar yadda suke yi a jihar Adamawa, a kodayaushe suna fafutukar samun manyan mukamai masu tsoka, shine abun da suke niyan yi idan ya samu shiga Aso Rock.
“Amma kamar yadda na yi wa yan Najeriya bayani, ba kimiyyar roka bane, wannan mutumin (Atiku) yana da yara 31 da ya haifa a cikinsa, 30 daga cikinsu balagaggu ne.
“Dukkanin wadannan balagaggun na son zama biloniya. Zai tatse albarkatun kasar nan sosai ko kuna so ko ba ku so, kawai ku fahimci gaskiyar magana kuma wannan ba abu ne da za mu iya daukarsa a wannan lokaci da muke ciki a yauwar Najeriya.”
Har ila yau, Achimugu ya ce ya fallasa badakalar tsohon ubangidan nasa ne domin hana yan Najeriya yin babban kuskure ta hanyar zabansa, rahoton Punch.