2023: Bayan Atiku, Tinubu ya Nemi ya Gana da Shekarau Ranar Laraba
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya gayyaci tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, zuwa taro a ranar Laraba, kwararan majiyoyi suka shaidawa Daily Nigerian.
Dan takarar shugaban kasar na APC ya gayyaci Mista Shekarau, wanda shine dan takarar sanata na jam’iyyar NNPP, zuwa taro domin zawarcinsa ya dawo jam’iyyarsa.
Daily Nigerian ta rahoto cewa Mista Shekarau ya riga ya cimma yarjejeniya da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar cewa zai koma jam’iyyarsu a nada shi shugaban kamfen na Arewa maso Yamma.
Sai dai mai magana da yawun Shekarau, Bello Sharada ya musanta wannan rahoton yana mai cewa an tattauna batun wurin taron Shura amma ba a amincewa da komawar Malam zuwa PDP ba.
Read Also:
Babban jigo a jam’iyyar PDP a Kano ya shaidawa Daily Nigerian cewa jam’iyyar ta fara shirin sauya tsare-tsarenta don maraba da Shekarau.
A cewarsa, mataimakin shuganan PDP na yankin arewa maso yamma, Bello Hayatu Gwarzo, ya sanar da manyan shugabannin jam’iyyar game da zuwan Shekarau da shirin tarbarsa.
Daily Nigerian ta samu sahihin rahoto cewa abokin takarar Tinubu, Kashim Shettima, da farko ya gana da Shekarau a ranar 8 ga watan Agusta amma majiyoyi sun ce “ba dai-daita ba”.
Duk da cewa wasu na kusa da tsohon gwamnan sun ce ya riga ya yanke shawarar komawa PDP, shi (Shekarau) – saboda ‘ganin ido’ – ya kira taron masu bashi shawara, kwamitin Shura, don su basu shawara.
Ana sa ran kwamitin za ta kammala rahotonta yau sannan a sanar da matakin da ta dauka a makon mai zuwa.
Dakaci karin bayani …