Yadda Attajiri ya Yanke Jiki Ya Fadi Bayan ya Gama Yabon Shugaban Masarautar Daular Larabawa
Wani faifan bidiyo mai ban tsoro ya nuna lokacin da wani Attajirin dan kasuwa ya fadi ya mutu a lokacin da yake jawabi a wani taro a kasar Masar.
Rahotanni sun nuna cewa Muhammad Al-Qahtani ya yanke jiki ya fadi bayan ya gama yabon shugaban Masarautar Daular Larabawa Mohammed bin Zayed.
Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin mutuwar Attajarin dan kasuwa daga kasar Sudiya Al-Qahtani ba.
Masar – Wani faifan bidiyo mai ban tsoro ya dauki lokacin da wani dan kasuwa ya fadi ya mutu a lokacin da yake jawabi a wani taro a Masar.
Read Also:
Rahoton 21Centurychronicle Rahotanni sun bayyana cewa, Muhammad Al-Qahtani, wani dan kasuwa daga kasar Saudiyya da ke zaune a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron kasashen Larabawa da Afirka da aka yi a birnin Alkahira a ranar Litinin din da ta gabata.
Al-Qahtani shi ne shugaban kwamitin gudanarwa na Kamfanin Al-Salam Holding Company kuma an ruwaito cewa ya rike mukamai da dama na girmamawa a matsayin jakadan fatan alheri.
Ya kasance yana magana ne a wurin taron, wanda aka gudanar Mai taken ” Nuna goyon baya ga nasarorin da shugaban Masar Abdel Fattah Al-Sisi ya samu”, a lokacin da ya fadi, kamar yadda Arabi21 ta rawaito.
Rahotanni sun ce ya marigayin yayi kalaman yabo ga Shugaban Masarautar Larabawa Mohammed bin Zayed kafin ya fadi a kasa. Abdullah Elshrif, dan kasar Masar ya sanar a shafin sa na Youtube cewa Al-Qahtani ya mutu ne bayan da jami’an tsaro suka dauke shi zuwa wani daki a wajen taron.
Kamfanin dillancin labaran Arabi21 ya bayar da rahoton cewa, taron ya samu halartar wakilan kungiyoyin kasa da kasa, shiyoyin Larabawa da kuma jakadu.
Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin mutuwar Al-Qahtani ba.