Bincike ya Nuna Yadda Auran Wuri ke yiwa Yara Mata Illa
Kungiyar Save The Children International ta ce auren wuri yana halaka fiye da yara mata 60 a ko wacce rana.
Kungiyar ta bayyana wannan rahoton ne a ranar yara mata ta duniya, inda ta bukaci a tseratar da su.
A cewar kungiyar, bisa kiyasi, a Najeriya ana yi wa mata kashi 44% aure kafin su cika shekaru 18.
Kungiyar Save the Children International ta ce auren wuri yana halaka fiye da yara mata 60 a ko wacce rana, kungiyar ta tallafa wa yara mata ta duniya ta bayyana hakan a ranar yara mata ta duniya.
Bisa kiyasi, ana aurar da 44% na yara matan Najeriya kafin su cika shekaru 18, wanda Najeriya tana daya daga cikin kasashen da su ka fi yin auren wuri a duk fadin duniya kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Kamar yadda Kunle Olawoyin, manajan sadarwa na Save the Children ya bayyana, ya ce dakyar a rage yawan auren wuri a Najeriya sakamakon tsaka mai wuya da mata suke rayuwa a ciki a halin yanzu.
Kamar yadda ya bayyana bisa ruwayar Vanguard:
“Sakamakon rikici, fadace-fadace, garkuwa da mutane, annoba da fatarar da ake rayuwa a ciki a Najeriya, mata da dama su na rayuwa cikin tsaka mai wuya wanda yake janyo su kasa karatu, ci da sha, su shiga cikin rashin tsaro da rashin samun damar amfana da kayan masarufi, kamar yadda rahoton halin da yara matan Najeriya suke ciki ya bayyana.”
“An kiyasta yadda fiye da mata 22,000 suke rasa rayukan su duk shekara sanadiyyar ciki da haihuwa saboda auren wuri, kamar yadda sabon binciken Save The Children ya bayyana a ranar yara mata ta duniya.”
“Sakamakon yawan auren wuri dake faruwa a duniya, yammaci da tsakiyan Afirka sun bayyana cewa mata 26 su ke rasa rayukan su kullum.
“Kudancin Asia su na ganin auren wuri yana zama sanadin mutuwa 2,000, a ko wacce shekara, kenan mutane 6 a ko wacce rana.Sannan arewacin Asia da Pacific su na samun mutuwa 650 a shekara sakamakon mutuwar mata 2 a ko wacce rana.”
Duk da dai anyi kokarin dakatar da auren wuri 80,000,000 a shekaru 25 da su ka gabata, ana ci gaba da samun nasarar hakan kafin annobar COVID-19 ta barke, wanda ta yi sanadin auren wuri da dama.
Saboda rufe makarantu da asibitoci, hakan ya janyo fatara ga mutane da dama, mata da dama sun fuskanci kalubale a lokacin.