Babu Aibi Akan Kiran ‘Black Friday’ – Malaman Kano ga Hisbah

Fatawar majalisar malaman Kano ta sha ban-ban da na hukumar Hisbah kan lamarin ranar Black Friday da aka haramta fadinsa a jihar Kano don wasu dalilai.

Yayinda Hisbah take ganin Juma’a babbar rana ce kuma bai kamata a alakanta ta da wani abun aibi ba ko yaya ne, majalisar malamai na da ra’ayin babu laifi.

Shugaban majalisar malamai, Malam Ibrahim Khalil, ya bayyanawa tashar rediyo, Freedom, cewa babu laifi cikin bikin ranar ‘Black Friday’.

“Tun asali amfani da kalmar ‘Black Friday’ ba ya nufin mummunan abu, hasalima yabo ne,” cewar Malam Khalil.

“Ba magana ce ta suka ba, in ka kalli tarihi, sai dai in mutum bai bincike abin da fadi ba.”

Malamin ya kara da cewa bai san dalilin hukumar Hisbah na daukar matakin hana amfani da kalman da tayi ba, kuma idan da sunan addini ne to babu gabar kamawa.

A cewar wani malamin addini, Sheikh Abubakar Baban Gwale, yace babu laifi, bal ranan halastacce ne.

“Batun wanda suka kirkiri bikin ranar ko kiranta da ‘Black Friday, ba za su sanya a haramta ta ba,” yace

“Shi yasa yawancin fatawar malamai itace, babu laifi mutum yaci moriyar ranar …amma kada ya sayi haramtattun kaya.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here