Daga Mahmud Isa Yola
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Ash-Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau ya gargadi masu yada jita jita a kafafen yada labarai wai cewa kungiyar Izala na takun saka da ‘yan Dariku.
Sheikh Bala Lau yana magana ne akan wasu rahotanni da cikin kwanaki biyun nan suke yawo a jaridu cewa wasu ‘yan Darika sun far wa Sakataren Kungiyar na kasa Sheikh Dr. Muhammadu Kabiru Gombe a Kaduna inda ya sha da kyar.
Bala Lau ya muzanta labarin ne a yau jumma’a a majalisin Tafsirin sa da ke Yola, inda yace babu kanshin gaskiya a cikin wannan rahoton, kuma wadanda suke yada rahoton suna yi ne don bibiyar kungiyar da sharri da makircin su.
Read Also:
“Tsakanin wurin tafsirin Sheikh Kabir Gombe da inda Sheikh Dahiru Bauchi yake akwai nisa sosai, babu wani abu da ya faru. Kungiyar Izala bata rigima da ‘yan darikar Tijjaniya ko wasu, sun san matsayin su, mun san matsayin mu” inji Sheikh Bala Lau.
Shehin malamin yace suna sane da wadansu sun sha alwashin farraka kungiyar Izala saboda matsayar da kungiyar ta yi a zaben 2019 da ya gabata. Yace babu shakka wadannan sune suke bibiyar kungiyar da sharri don su ga sun zubar da kiman shugabannin ta a idon al’umma.
Sheikh Bala Lau yayi kira ga masu yada rahotannin su ji tsoron Allah, su kasance masu yada gaskiya ba sharri ba. Yace babu amfanin yada abunda bai faru ba a cikin al’umma, kuma Qur’ani yayi gargadi akan hakan a wurare da dama.
The post Babu Rigima Tsakanin Izala Da Darika — Sheikh Bala Lau appeared first on Daily Nigerian Hausa.