Babu Sulhu Tsakaninmu da ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Jahar Kaduna
Matsalar tsaro na cigaba da kwasan rayukan mutane a jahar Kaduna.
A rana guda, gwamnatin jahar tayi alhinin kisan mutane sama da 20.
Gwamna El-Rufa’i ya bayyana cewa babu sulhu tsakaninsa da yan bindiga.
Gwamnatin jahar Kaduna ta bada rahoton kisan mutan jahar 23 da yan bindiga sukayi a kananan hukumomi biyar na jahar a rana guda kacal.
Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata. A cewar Aruwan, yan bindigan sun kai wadannan hare-hare ne a iyakokin jahar da wasu jahohin dake makwabta.
Jawabinsa yace: “Sakamakon matsalar tsaron da jahar ke fama da shi cikin sa’o’i 24 da suka gabata, gwamnatin jahar Kaduna ta samu labari daga hukumomin tsaro cewa an kashe mutane 23 a hare-haren da aka kai kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi da Kauru.”
Aruwan yace mutum 10 aka kashe a karamar hukumar Birnin Gwari kadai.
Read Also:
Sune: Abdu Hasan; Sufyanu Musa; Faisal Zubairu; Abdullahi Hasan; Ali Abdu; Rabiu Aliyu; Zubairu Yau; Bukar Yusuf; Mamman Ibrahim da Dankande Musa.
Wadanda suka jigawa kuwa sune Baushi Alu, Rabe Sani da Usama Sani. A karamar hukumar Igabi kuwa, Aruwa ya ce yan bindigan sun bindige Dayyabu Yahuza.
A karamar hukumar Giwa, Aruwan yace “yan bindiga sun kai hari kauyen Janbaba, inda suka kashe wani Yakubu Sule,”.
A karamar hukumar Kauru kuwa, Aruwa ya ce mutum biyar aka kashe wanda suka hada da Danlami Sunday; Abbas Abou; Sati Yakubu; Shaba John da John Francis a kauyen Kishisho.
A karamar hukumar Chikun, Aruwan ya bayyana cewa an kashe Habila Ibrahim; Samaila Audu; John Musa; Birnin Aboki da Ali Aboki, a kauyen Gwagwada-Kasaya, yayinda aka kashe Bitrus Joseph a kauyen Agwa.
Aruwan ya kara da cewa an kashe dan bindiga daya, lokacin da mutan garin suka taso musu.
Gwamnan jahar Kaduna, a jawabin, ya yi alhinin wannan hare-hare, yayinda yake jajantawa wadanda sukayi rashi kuma yake addu’a ga wadanda suka jigata.