Kotun Musulunci ta Jahar Kano ta ki Bada Belin Abduljabbar Nasir Kabara

 

Babbar kotun musulunci ta Jahar Kano da ke arewacin Najeriya ta ki amincewa da bayar da belin Malamin addinin nan Sheik Abduljababr Nasir Kabara.

Cikin wani zama da aka yi a ranar Alhamis, alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, ne ya ki amincewa da bukatar da Barista Umar Muhammad wanda shi ne ke jagorantar lauyoyin Abduljabbar ya gabatar.

Gabanin fara shari’ar lauyoyin Abduljabbar sun bukaci da a ba su kwafin shari’ar, tare da kira ga masu kara da su gabatar da shaidunsu a zama na gaba domin a fara sauraro.

Alkalin ya dage saurar karar zuwa ranar 14 ga watan October na gobe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here