Baɗala: Jami’ar Obafemi Awolowo ta Sallami Lakcara Mai Koyar da Turanci a Jami’ar
Jami’ar Obafemi Awolowo University, da ke Ile-Ife ta sallami wani lakcara mai suna Dr Adebayo Mosobalaje.
An kore Dr Mosobalaje ne bayan samunsa da laifin badala da wata daliba a makarantar.
Majalisar kolin Jami’ar ta ce an kafa kwamitin bincike kuma sun tabbatar da laifin don haka aka kore shi kamar yadda dokar jami’ar ta tanada.
Ibadan, Oyo – An sallami Dr Adebayo Mosobalaje, malami a tsangayar koyar da harshen turanci a Jami’ar Obafemi Awolowo University, da ke Ile-Ife saboda badala, Daily Trust ta rawaito.
Vanguard ta rawaito cewa Mahukunta a makarantar sun amince da korarsa daga aiki ne bayan an same shi da laifin cin zarfin wata daliba a jami’ar.
Read Also:
Mai magana da yawun jami’ar, Abiodun Olarewaju ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
“A yunkurinta na kawar da dukkan wani nau’i na badala, cin zarafi da tursasawa a jami’ar, mahukunta a Jami’ar Obafemi Awolowo University, Ile-Ife, ta sake korar wani lakcara da aka samu da laifin cin zarafin daliba.
“An cimma matsayar korar Dr Adebayo Mosobalaje na tsangayar koyar da harshen turanci ne yayin taron majalisar kolin jami’ar na karshe da aka yi a ranar Talata 7 ga watan Satumban 2021.
“Bayan tattaunawa sosai kan rahoton kwamitin koli na jami’ar, wacce ta yi bincike kan zargin badalar da ake yi wa Mosobalaje, Jami’ar ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wani nau’in badala ba hakan yasa jami’ar ta dauki matakin kamar yadda ya ke a dokarta.”