Gwamnan da ya ke Korar Ma’aikata Bai da ta Cewa a Kai na – Gwamna Ortom ga Gwamna El-Rufa’i
Gwamnan jahar Benuwai, Samuel Ortom, ya sake yi wa Nasir El-Rufai raddi.
Ortom ya yi martani ne bayan El-Rufai ya zarge shi da rashin biyan albashi.
A cewar Ortom, gwamnan da ya ke korar Ma’aikata bai da ta-cewa a kan shi.
Gwamnan jahar Benuwai, Samuel Ortom, ya soki takwaransa na Kaduna, Nasir El-Rufai, game da kalaman da ya yi kan batun tsaro, inda ya yi masa raddi.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Samuel Ortom ta bakin sakataren yada labaransa, Terver Akase ya kuma maida wa gwamna Nasir El-Rufai martani.
Terver Akase ya yi kaca-kaca da gwamnan jahar Kaduna, ya zarge shi da nuna kiyayyar addini da kabilanci.
Read Also:
“Gwamnan da ya dauko musulmi a matsayin mataimakiyarsa, a jahar da kiristoci suke da jama’a masu yawa, ba zai iya yin kiran a zauna lafiya ba.” Inji Akase.
“El-Rufai ya duro kan Ortom ne saboda fadar shugaban kasa ta ga farinsa, bayan ya samu sabani da manyan Aso Rock, ya na so ya yi amfani da gwamna Ortom.”
“Ta ya ya shawo kan matsalolinsa a jahar Kaduna? Mutumin nan ya soki kusan kowane babba a Najeriya har da Umaru Musa Yar’Adua da Olusegun Obasanjo.”
Ya ce: “Bamu manta da irin munanan abubuwan da ya fada a lokacin mulkin Goodluck Jonathan ba. Ya ci wa shugaban kasa mutunci, ya goyi bayan ‘yan ta’adda.”
Akase bai musanya mai gidansa ba ya biyan albashi ba, sai dai ya ce bai raba ma’aikata daga aikinsu ba. “El-Rufai bai da hurumin da zai yi wa wani gori a kan biyan alhashi da walwalar ma’aikata.
Wannan gwamna ne da ya kori ma’aikata 4, 000 haka kurum.” “Kamata ya yi, ya ji kunyar kan shi. Ina alkawuran da ya rika yi wa jama’ar Kaduna a 2015?”