Sokoto: Bakuwar Cuta ta Fara Kashe Mutane a Jahar

 

Gwamnatin jahar Sokoto ta fidda wata sanarwa mai bayyana barkewar wata sabuwar cuta a wani fannin jahar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun gwamnan jahar ta bayyana cewa mutane hudu sun mutu daga cutar.

Ta kuma nuna adadin mutanen da suke asibiti a halin yanzu suna karbar magani sun haura 20.

An tabbatar da mutuwar wasu mutane hudu sakamakon wata baƙuwar cuta da ta addabi yankin Helele na cikin jahar Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal wanda ya tabbatar da bullar cutar a cikin wata sanarwa da shi da kan sa ya sanya hannu, ya ce a yanzu haka wasu 24 na karbar kulawa a asibitoci daban-daban a fadin jahar.

Gwamnan ya ce an kirkiri wani kwamiti da nufin bincikar cutar tare da gano maganinta da rigakafin ta.

Sanarwar ta karanta:

”Gwamnan jahar Sokoto, Rt. Hon Aminu Tambuwal, CFR Mutawallen Sokoto, a madadin gwamnati da daukacin jama’ar jahar, ya nuna alhini da ta’aziyya ga iyalai da dangin ‘yan uwanmu, wadanda suka mutu,”

A cikin sanarwar, gwamnan ya nuna alhini ya kuma yi wa ‘yan uwan wadanda suka mutu ta’aziyya.

Dangane da bincikar tushe da asalin cutar, sanarwar ta ce:

“A halin yanzu Gwamnatin Jaha ta tashi da kwamitin kwararru, karkashin jagorancin Kwamishinonin lafiya da na muhalli na jahar, da nufin bincikar cutar da gano maganinta da rigakafin ta.

“Bugu da kari, Gwamnati ta dauki nauyin kula da mutanen da ke fuskantar kulawar likita sakamakon rashin lafiyar kuma tana yi musu fatan samun sauki cikin gaggawa tare da komawa ga danginsu da ‘yan uwansu.

“Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal yayin da yake kira ga nutsuwa, yana umartar jama’a da su kiyaye dabi’u na tsafta da kulawa kuma su dage da addu’o’in neman taimakon Allah a wannan lokaci na kalubale.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here