Bam ya Tashi a Jahar Kogi
Kogi- Akalla mutum uku ake fargabar sun rasa rayuwarsu kuma wasu da dama suka jikkata yayin da wani Bam ya tashi a Kabba, jihar Kogi da daren ranar Laraba.
Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9:45 na dare lokacin da mutane ke tsaka holewarsu a wani gidan Giya.
Wata majiya ta bayyana cewa:
“Na ji wata ƙara mai tsanani ƙarfi kuma babu nisa daga inda nake, nan take na nufi wurin dom gane wa idona, na ga gawar mutum uku kwance yayin da waɗan da suka jikkata an kai su Asibiti.”
“Mutanen da suka ji rauni an kai su babban Asibitin St. John da ke Kabba, domin ba su kulawa.”
Read Also:
Haka nan, wani ɗan Acaba wanda ya bayyana sunansa da Dele, ya ce: “Bam ne ya tashi saboda ƙarar ta yi tsanani, mutane sun mutu, wasu sun jikkata. Na ga yadda jami’an tsaro suka ɗauki mutanen zuwa Asibiti a Kabba.”
Wane matakin jami’an tsaro suka ɗauka?
Sai dai kwamishinan yan sanda reshen Kogi, Mista Edward Egbuka, ya shaida wa hukumar dillancin labarai NAN cewa rahoton da suka samu ya nuna tukunyar Gas ce ta fashe ba Bom ba.
Ya ƙara cewa a halin yanzun Jami’ansa na kan aiki kan lamarin kuma zai fitar da cikakken bayani game da fashewar bayan kammala bincike.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa irin wannan harin ya faru a jihar Taraba a watan da ya gabata, kuma daga bayan kungiyar ISWAP ta ɗauki nauyin kai harin.