An Kama Kansila Dauke da Bindiga Kirar AK-47 a Jahar Kaduna

 

Jami’an tsaro sun kama wani mutumi yana rike da bindiga a yankin dajin Galadimawa a Kaduna.

Bincike ya nuna wannan Bawan Allah da aka cafke yana kan kujerar Kansila ne yanzu a garin Soba.

Ana tunanin har zuwa yanzu Hon. Abdul Adamu Kinkiba yana tsare a hedikwatar ‘Yan Sanda a Kaduna.

Kaduna – Jami’an tsaron da ke aiki a yankin Galadimiwa, karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna sun yi ram da wani Bawan Allahi, Abdul Adamu Kinkiba.

Daily Trust ta ce Hon. Abdul Adamu Kinkiba Kansila ne a karamar hukumar Soba da ke jihar.

Honarabul Abdul Adamu Kinkiba ya fada hannun jami’an tsaron ne a kusa da wani sanannen gungu da ‘yan bindiga su ke fakewa, su na addabar mutane.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Kansilan yana rike da wannan bindiga ta AK-47 ne a kan babur, a lokacin da wasu dakarun tsaro suka ci karo da shi.

Da ake yi masa tambayoyi, Abdul Kinkiba ya shaidawa jami’an tsaron cewa wani mutum ne ya ba shi bindigar, amma ya ce ba zai iya tuna sunan mutumin ba.

Yadda abin ya faru – Majiya

“Ya ce an fada masa cewa bindigar ta tawagar wani ce. A cewarsa, an fada masa ya zo ya tsaya da zarar an wuce gadar da ke daf da dajin Galadimawa.”

Wannan wuri ne da miyagun ‘yan bindiga suke samun mafaka, an fada masa cewa wani mutum zai zo nan ya karbi bindigar daga hannunsa.” – Majiya.

Kansilanmu ne inji Soba LG

Shugaban karamar hukumar Soba, Honarabul Suleiman Yahaya Richifa ya tabbatar da wannan labari, ya ce babu shakka wanda aka kama Kansila ne a garinsu.

Injiniya Suleiman Yahaya Richifa ya ce Abdul Kinkiba shi ne Kansilan gundumar Kinkiba a Soba.

Amma Richifa ya ki cewa uffan bayan hakan, ya nuna samun wannan labarin ya matukar girgiza shi, ya ce ba zai iya magana a kan rahoton a halin da ake ciki ba.

Kawo yanzu, an wuce da wannan mutumi zuwa babbar hedikwatar ‘yan sanda da ke garin Kaduna, domin amsa tambayoyi inda za a binciki lamarin da kyau.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here