Bama Son Rasa ‘Ya’yanmu Amma ba za mu Tursasa Kowa Zama ko Ficewa Daga Cikinmu ba – Abdullahi Adamu

 

Kamar yadda yake a tsarin siyasar Najeriya ana yawan samun sauye-sauyen sheka a duk lokacin da guguwar zabe ta kado.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce basa son rasa ‘ya’yansu amma ba za su tursasa kowa zama ko ficewa daga cikinsu ba.

Adamu ya ce duk wani dan jam’iyya balagagge ne wanda ya mallaki hankalin kansa, don haka yana da damar daukar duk hukuncin da yake ganin shi yafi dacewa.

Nasarawa – Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Adamu ya ce jam’iyyarsa bata son rasa kowani mamba amma ba za ta iya tilastawa kowa ci gaba da zama a cikinta ba.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar bayan ya ziyarci gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Mohammed, a gidan gwamnati da ke Lafiya, Adamu ya ce yanzu lokaci ne na sauya sheka a bangaren siyasar kasar.

Shugaban jam’iyyar ya ce yan siyasa mutane ne da suka mallaki hankalinsu wadanda za su iya yiwa kansu zabi na abun da suke so, jaridar The Cable ta rahoto.

Ya ce:

“Ba ma son rasa kowani mamba amma idan wani mamba ya ga yana son barin jam’iyyar ba tare da neman mafita ba, ba za mu tilastawa kowa tsayawa ko barin jam’iyyar ba.

“Batun sauya sheka, akwai lokaci na hakan a siyasa musamman a kasashe masu tasowa, kuma ba sabon abu bane a Najeriya.

“Duk wani mamba na wannan jam’iyyar ya mallaki hankalinsa kuma idan balagagge ya yanke hukunci, to ko dai ka gamsar da shi, idan kuma hukuncin bai yi maka dadi ba kuma ya aikata abin da yake so, sai ka bar ma Allah wanda ke tsara komai.”

Channels TV ta kuma rahoto cewa Adamu ya ce jam’iyyarsa na aiki don lashe babban zaben da za a yi a watan Fabrairun 2023.

Ya ce:

“Kan batun lashe zabe, muna aiki don yin nasara. Da izinin Allah, za mu lashe zaben.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here