Bama Samun Damar Yin Karatun Boko – Sarkin Kutare
Daga Hannatu Suleiman Abba
Sarkin kutare a jahar Kano malam isiyaku Muhammad ya bayyana cewa , rukunin su a jerin masu bukata ta mussaman a jahar Kano sun fi yawan a bangare rashin samu damar yin ilimi Boko a jahar.
Malam Isiyaku yayi wannan jawabin ne a lokaci da Yake bayyana irin kalubale da suke fuskanta a matsayin su na masu larurar cutar kuturta a jahar, Wanda yace dayawan su rashin ilimi Boko ya hana a dama dasu a bangarori da dama na masu bukata ta mussaman a jahar.
A son gani masu larurar cutar kuturta su samu damar yin karatun Boko a jahar kano,na kafa makaratar koyar da su daukar darusa a cikin gidana da yamma,kafin daga bisa Hukumar bayan Mika korafi ga Hukumar ilimi ta jahar, a sashin makarantar koyar da manya karatu na Yaki da jahilci ,Suka bamu guri a kusa da makabarta dake unguwar Tudun Wada,Amma tun da aikin hanya ya biyo ta Kan gurin aka tashe mu,har Yanzu ba a Samar Mana da wani guri ba,tare da dakatar da biya mu alawus din dubu 6 a wata da take Yi.
Masu larurar cutar kuturta suna da hazaka akan duk abinda suka saka a gaba, mussaman idan akayi la’akari da cewa kwakwalwar su na aiki, matsalar Yan yatsa ne,shima ana iya rike alkalamin rubutu dashi.
Read Also:
Gwamnati jahar Kano,ta ware wa saura masu bukuta ta mussaman makarantun karatu Wanda a cikin su har da masu matakin farfesa mussaman masu larurar ji da gani,da masu matsalar laka da sauransu, Amma mu ba inda zamuje a karbe mu sabida tsangwama da Kuma yadda al’umma ke kallon larurar ta mu.
Mal. Isiyaku Muhammad ya Kara da cewa,Daya daga cikin dalili da yasa na Zama sarki su ,Yana da nasaba da samun shaidar Kamala karatun sakandari da nayi kafin larurar ta bayyana a jiki na,duk da cewa nayi niyyar cigaba da karatu a kwaleji sa’adatu Rimi Amma duba da irin kalubale da Kuma rashin tallafi yasa na tsaya a Haka. Ko a yanzu waziri na bazai iya karatu ko iya rubuta sunan sa ba,Wanda Haka ba karamin barazana ne ga mu masu larurar cutar kuturta ba.
Rashin karatun Boko a cikin mu yana shafar har Ya’yan mu sabida Basu ga muna Yi ba.
Hakazalika,Ina yawan zubar da hawaye indai na kallin fuska ta a mudubi,Na ga girma ya Fara cimmin Amma har Yanzu jama’ar da nake shugabanta basa cikin wayenda ake dama wa dasu a fannin ci gaban rayuwa na zamani, Domin ko a kwananan gwamnati jahar Kano ta dibi ma’aikata Bangare masu bukata ta mussaman Amma Kuma bangare mu ba kowa sabida bamu da kowa da yayi ilimi Boko da za’a a dama dashi a al’amuran yau da gobe a cikin al’umma.
Sarkin masu larurar cutar kuturta a jahar kano Malam Isiyaku muhammad ya Bukaci gwamnati da kungiyoyi masu zaman Kansu da su taimaka wa masu larurar a fanni ilimi domin shine haske da Zai magance matsalar su a rayuwa.