Bogi da na Gaske: Hanyoyi 5 da zu ku bi Wajen Bambance Kudaden

 

Kowa na son kudi, hakazalika a kullum ana kashe kudaden da ba adadi, wannan yasa kudi ke da matukar daraja a idon kowane dan adam mai rai saboda dasu ne a ke cinikayya a kowane lokaci.

Kamar yadda aka sani, kudade ana samar dasu ne ta wasu hanyoyi masu matukar sarkakiyar dokoki da gwamnatoci ke ke samar wa, wannan yasa ba kowa ne zai ji a ransa zai buga kudi ba.

Sai dai, a bangare guda, akan samu wasu bata-gari da ke kera kudaden karya, wanda hakan babban kalubale ne ga tattalin arziki da ma mu’amala tsakanin jama’a.

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta tattaro bayanai daga jaridar The Nation kan yadda mutum zai gane kudaden bogi don kaucewa cutarwar ‘yan damfara masu jirkita Naira, kudin Najeriya.

1. Duba wata dan zare a jikin Naira

A jikin Naira, akwai wani siririn zare a gefe guda wanda ya gangaro daga sama har kasa. Za ku ga manne wannan zare aka kasancewar ba hade yake da takardar da aka buga kudin ba.

A kudaden bogi kuwa, sam-sam babu wannan zare, ko ma dai akwai, to lallai zaku ga irin na jikin Naira ba ne saboda zaku ga an buga hoton zaren ne a jikin takardar kudin na bogi.

2. Tsoma Naira cikin ruwa ko wani nau’in ruwa-ruwa

Domin gane kudin bogi, jika kudin da ruwa sannan ku murza a jikin hannunka da kyau, maukar na bogi ne, to launukan jikin kudin zai goge kana ya manne a hannayenku.

Sabanin wannan, kudin gaske bai wankuwa domin an tsoma shi a ruwa ko wani nau’in abu mai ruwa-ruwa ko da kuwa man fetur ne.

3. Yi amfani da madubin duba-rudu

Musamman gudun duba N1000, ba a iya ganin wasu zane-zanen da ke jikin kudi sai an yi amfani da madubin da zai taimakawa ido ya gani.

Domin gane hakan, ku nemi madubin duba kananan abubuwa domin ku gane kudin bogi da na gaske ba tare da bata lokaci ba.

Ku gwada wannan da gudan N1000, za ku ga wasu rubutun masu launi ruwan dorawa an rubuta N1000 a wasu sassan kudin.

4. Duba likakkiyar takardar zinare

Takardar N1000 tana da wata takardar zinare like a gefen dama kusa da sa hannun gwamnan CBN. Ya kamata ku sani cewa idan kuka kankare wannan zubin zinare, idan kudin bogi ne zai goge.

Don haka idan zabin lambobin sama na iya zama masu wahala, kuma kuna rike da gudan N1000, za ku iya kokarin kankare wannan alama don gane kudin gaskiya.

5. Takarda da ingancin launi

Yayin da ake yin jabun takardu irin na yau da kullum, kudin gaske ana yinsu da takarda ta musamman.

Daga murza takardar kudi, za ku gano cewa takarda ce kawai. Launukan jabun kudi, a bayyane suke. Zane-zanen da ake yi na jabu sun fi zama bau, kyallinsu kuma wani lokacin ya fiye duhu sabanin kudin gaske.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here