Ban Taɓa Addu’a Kan ALLAH Yasa na Zama Gwamna ba – Gwamnan Jahar Oyo

 

Seyi Makinde, gwamnan jahar Oyo ya ce bai taba yin addu’ar Allah yasa ya zama gwamna ba.

Makinde ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi lokacin da ya ke tarbar mambobin FIBAN da BCOS a gidan gwamnati.

Mambobin kungiyoyin biyu sun ziyarci gwamnan ne domin neman ya saka baki kan wasu matsaloli da suke fuskanta.

Gwamna Seyi Makinde na jahar Oyo, a ranar Alhamis ya ce bai yi addu’ar ya zama gwamna ba a 2019, inda ya ce kawai shi kawai fatansa shine Allah ya zartar da ikonsa a jahar, Daily Trust ta ruwaito.

Makinde ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tarbar mambobin Kungiyar masu watsa labarai masu zaman kansu, FIBAN, daga Kungiyar masu watsa labarai na jahar Oyo, BCOS, a gidan gwamnati da ke Agodi, Ibadan.

Gwamnan ya yi alkawarin zai duba batun sallamar wasu mambobin kungiyar da aka yi daga aiki inda ya ce gwamnatinsa ba za ta rika rufa-rufa ba kuma za ta yi tafiya tare da kowa.

Ya kuma yi alkawarin saka baki kan matsalolin da ke tsakanin mambobin BCOS da FIBAN cikin makonni hudu.

“Da na ke addu’a a game da zaben 2019, ban yi addu’ar Allah yasa in zama gwamna ba, ni dai addu’ar da na yi shine Allah ya zartar da ikonsa a Jahar Oyo. Don haka, na san cewa kadarar Allah ne, Zai kawo wadanda za su tabbatar da abinda ya kaddara, daya daga cikinsu shine Sanata Monsurat Sunmonu.

“Yanzu na fara jin korafin ku. Idan da na san wannan shine abinda za mu tattauna, da na tuntubi Prince Dotun Oyelade ya zo taron. Ina maimaitawa, ban san da wannan matsalar ba. Dukkan mu muna kuskure, Allah ne kadai baya kuskure,” wani sashi cikin jawabin Makinde.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here