Wannan tattaunawa ce da jaridar Premium Times ta yi da tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Sunan Janar Ibrahim Babangida ya fara fitowa a duniya, tun a ranar 13 Ga Fabrairu, 1976, ranar da abokin sa Kanar Bukar Suka Dimka ya kashe Shugaban Kasa na mulkin soja a lokacin, Janar Murtala Ramat Mohammed wajen karfe 8:30 na safiyar ranar.

Bayan da Dimka ya kashe Murtala, sai ya zarce Gidan Radiyon Tarayya da ke Lagos, inda ya fara yin sanarwar ya yi juyin mulki. Sai dai kuma ya na cikin yi wa ‘yan Najeriya jawabi, sai Babangida ya darkaki gidan radiyon ya na jagorantar rundunar da aka tura ta murkushe Dimka.

Babangida ya ritsa Dimka a gidan radiyo, kuma ya yi masa hilar da ya hana shi ci gaba da gudanar da jawabin kwace mulki da ya fara. Babangida ya hana Dimka yin nasara, amma kuma bai kamu ba, saboda ya tsallake ya gudu a lokacin. Sai daga baya aka kama shi.

Tun daga waccan rana ce zakaran Babangida ya yi carar da har sai da ta kai shi ga shugabancin kasar nan.

Kwanaki kadan kafin ya cika shekaru 77 a duniya. Jaridar THE CREST ta samu zantawa da shi a gidan sa da ke Minna, inda ya yi bayani kan batutuwa da dama, kamar yadda za ku karanta, bayan PREMIUM TIMES ta samu amincewar The Crest ta fassara tattaunawar.

A ranar 24 Ga Yuli aka yi hirar da shi, a lokacin ya na saura wata daya ya cika shekaru 77 a duniya. Ya yi magana kan batutuwa da dama banda guda daya, shi ne sabanin da ya shiga tsakanin sa da Muhammadu Buhari, shugaban kasa na yanzu, wanda Babangida ya yi wa juyin mulki a wancan lokacin.

TAMBAYA: A yanzu ka cika shekaru 77, mene ne babbar nasarar ka ko kuma cikas da ka samu a rayuwa?

IBB: To na farko dai zan fara da cewa a lokacin da aka dauke ni aikin soja a matsayin matashin jami’in soja a Makarantar Koyon Aikin Soja ta Indiya. A lokacin ina cike da kuzarin bauta wa kasa ta.

Na biyu kuma a lokacin da ka ke aikin kishin bautar kasar ka, za ka ci karo da mutane iri daban-dadan domin a taimaka a kare lafiya da rayukan jama’a da dukiyoyin su. Babbar nasara a lokacin ita ce wai ni din nan, Manjo Babangida a lokacin sai ga ni ina jagorantar bataliyar sojoji 500 da ke a karkashi na.

Kenan, dole ka damu da su, ka kuma damu da yadda za ka yi kokarin ganin sun amince da kai, su na da yakinin cewa a matsayin ka na jagoran su, ba za a fita yaki ka kai su inda za a baro gawarwakin su a can ba. Ina farin cikin yadda na rika cudanya da su, ina ba su horo har ma ina cin abinci tare da su.

Har wasa muka rika yi tare da su, su ka yi amanna da ni sosai. A duk lokacin da suka ji za mu fita yaki, ko kadan ba za ka ma ga alamar fargaba a zukatan su ba.

TAMBAYA: Guda nawa daga cikin wadannan bataliya da ka rike ke tare da kai a yanzu?

IBB: A gaskiya ba su da yawa fa. Amma akwai kalilan, kuma tsufa ya kam masu sosai. Ba ma za ka iya gane su ba idan ka gan su.

Amma wadanda suka san ka sosai su na cewa ko bayan shekara 20 idan ka ga abokan da ka yi aikin soja da farko tare da su, ka kan shaida su, kuma ka kira sunan mutum a nan take. Shin ya aka yi ka iya gane mutane haka?

A lokacin da muke tasowa cikin aikin soja, an koya mana wani salon tantance mutane, inda za ka hardace sunan sojoji, sunan matan su da sunayen ‘ya’yan su. Har gasa mu kan yi don a ga wanda ya fi yin hardar rike sunaye da yawa. To daga nan ne rike sunayen mutane ya zame min jiki.

TAMBAYA: To bari dai mu shiga batutuwa muhimmai tukunna. Abokan aikin ka da dama, har da Benjamin Adekunle sun dauke ka dan siyasar soja. Me za ka ce?

IBB: Ai ka ga dai ni ban ma taba rike wani mukami na soja a lokacin da za a ce ya shafi nau’in siyasa ba.

A lokacin da muke mulkin soja kuma, ai mu na da ministoci da gwamnoni, wadanda muke kallon mukamai na siyasa suke rike. To ka ga a irin wannan na yin aiki da mutane da yawa, kuma na yi abokai da dama, wadanda za mu je yawo tare, mu halarci taruka sosai duk a tare.

TAMBAYA: Shin za a iya jera siyasa kafada da kafara da aikin soja kuwa?

IBB: Ni ina ganin za a iya yin haka domin su sojoji ai su na karkashin mulkin dimocradiyya ne. Saboda tun a soja an mana horo kuma mun horu da cewa mu tari mutuwa gadan-gadan, babu maganar mu tsaya mu yi aiki da hankali ko tunni.

TAMBAYA: Yallabai abin da ya sa na kawo maka batun kasancewar soja tsoma kafa a siyasa, shi ne kusan duk wani juyin mulki da aka yi, da hannun ka a ciki. Ko ba haka ba ne?

Lallai haka ne.

TAMBAYA: Me ya ke jan hankalin ka tun daga juyin mulkin 15 Ga Janairu, 1966?

IBB: A lokacin ai ka ga ina karamin jami’in soja. Ba da ni aka shirya yakin ba tun da farko. Daga baya, bayan an yi juyin mulki a Kaduna, an rika sanya mu wasu ayyuka a lokacin.

TAMBAYA: Kamar wace rawa ce ka taka lokacin?

IBB: Na jagoranci wata runduna, amma aikin mu shi ne mu fita domin mu kare wani yanki da ake ganin tashin hankali ka iya barkewa ko a Lagos, Kaduna ko Ibadan.

TAMBAYA: Juyin mulkin da Dimka ya gigita kasar nan matuka. Ya ka ji a lokacin?

IBB: Ba zan manta a lokacin Kanar Ibrahim Taiwo ya na gaba da ni. Wanda ya yi gwamnan Kwara, kuma aka kashe shi a juyin mulkin 13 Ga Fabrairu, 1976 din da Dimk suka shirya.

Wata rana sai ya ga ina karanta wani littafi, mai suna ‘Yadda ake shirya juyin mulki.’ Sai ya ce min “Ibrahim, ka tabbatar cewa ka karance littafin kaf, kuma ka tabbatar ka hardace babi na 23 a cikin kan ka.

TAMBAYA: Me wannan babi na 23 ya kunsa?

IBB: Wannan babi ya na magana ce kan sakamakon abin da zai samu wanda ya shirya juyin mulki amma bai yi nasara ba. Ya ce min, ka tuna, idan ba ka yi nasara ba, to kashe ka fa za a yi. Ya ce min ka san abin da babin ya kunsa, domin idan ma ka shirya juyin mulki ba ka yi nasara ba, to kwanan ka ya kare.

TAMBAYA: Kuma sai wannan gargadin bai shiga zuciyar ka ba ko?

IBB: Ai bai shiga zuciya irin wannan gargadin, sai ma ka kara samun kwarin guiwa kawai. Domin za ka rika kallon kan ka a matsayin wanda ke sadaukar da ran sa kan bauta wa kasar sa. Sannan kuma za ka kalli kan ka cewa ga wani abu da ake aikatawa ba daidai ba. Sai kuma ka raya a zuciyar ka cewa za ka shiga ka gyara.

TAMBAYA: To amma tunda har ka san hukuncin kisa ne a kan wanda ya shirya juyin mulki bai yi nasara ba, shin ba ka tunanin shirya juyin mulki kamar kashe kan ka ne da kan ka?

IBB: A’a. Wannan karfin hali ne da kuma taurin rai da kuma taurin kai.

The post Ban taba nadamar abin da nayi a aikin soja ba – IBB appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here