Ban Taɓa Yarda da NATO ba – Trump

 

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yana nazarin yiwuwar janye Amurka daga ƙungiyar tsaro ta NATO, kamar yadda ya bayyana a wata hira da ya yi da jaridar The Telegraph.

Jaridar ta ruwaito cewa Trump ya bayyana ƙungiyar a matsayin ‘kyanwar lami’ yana mai cewa ba ta da ƙarfi kamar yadda ake tsammani. Haka kuma ya yi iƙirarin cewa Britaniya ba ta sojojin ruwa masu ƙarfi

Da aka tambaye shi ko zai sake duba matsayar Amurka kan kasancewa cikin NATO bayan rikicin Gabas ta Tsakiya, Trump ya ce: “Eh, zan iya cewa ya wuce ma a sake tunani…”

Ya ƙara da cewa: “Ban taɓa yarda da NATO ba. Na daɗe da sanin cewa ƙungiyar ba ta da ƙarfi, kuma shugaban Rasha, Vladimir Putin ma ya san haka.”

Trump ya kuma soki Birtaniya, yana cewa: “Ba ku da rundunar ruwa mai ƙarfi. Kun tsufa, kuma kuna da jiragen da ba sa aiki yadda ya kamata,” yana nuni da halin da rundunar ruwan ƙasar ke ciki.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here