Na ji Bakin Cikin Dakatar da Sanata Abdul Ningi – Gwamna Bala
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammad ya nuna damuwarsa kan matakin da majalisar dattawan Najeriya ta ɗauka na dakatar da sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawan ƙasar, Sanata Abdul Ahmed Ningi tsawon wata uku.
A ranar Talata ne majalisar ta dakatar da sanatan bayan zarginsa da zubar wa majalisar kima, a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya yi zargin cewa majalisar ba ta gano inda wasu kuɗi har tiriliyan uku suka shiga ba a kasafin kuɗin kasar.
Bayan dakatar da shi ne kuma, sanatan ya ajiye muƙaminsa na shugaban ƙungiyar sanatocin arewacin ƙasar.
Read Also:
Yayin da yake jawabi a taron majalisar zartaswar jihar a fadar gwamnati, gwamna Bola Mohammed ya ce ya ji takaicin dakatar da Sanata Ningi da majalisar dattawan ta yi.
” Haƙiƙa, jiya na ji bakin cikin dakatarwar da majalisar dattawan ƙasar nan ta yi wa ɗaya daga cikin jajirtattun sanatocin da muke da su a Bauchi, saboda faɗar gaskiya, saboda kawai ya tsaya a kan gaskiya,” in ji gwamnan na jihar Bauchin.
Gwamman Bala Mohammed – wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, ya kuma ce “Tabbas ban san abin da za mu yi ba, amma za mu tattauna da shi don ganin abin da ya kamata mu yi don taimaka masa, saboda ina goyon bayan duk abin da yake yi, kuma wannan shi