Shugabannin Bankuna Sun Bayyana Goyon Bayansu Kan Dage Ranar Daina Amfani da Tsofaffin Kudi
Ranar Alhamis kwamitin majalisar wakilai ta zanna da shugabannin bankuna a Najeriya.
Majalisa ta gayyaci gwamnan CBN, Godwin Emefiele, amma yayi kunnen uwar shegu ga gayyatar.
Gwamnatin shugaba Buhari ta ce tana kan bakanta, ba zata dage ranar daina amfani da Naira ba.
Abuja – Mambobin majalisar wakilan Najeriya sun yi ganawa da shugabannin bankunan dake Najeriya kan lamarin sabbin kudin Naira da karewar wa’adin tsaffin kudi.
Read Also:
Kwamitin da majalisa ta nada na musamman ta shiga zaman da shugabannin bankunan ne ranar 26 ga watan Junairu, 2023.
TVC ta ruwaito cewa taron ya gudana ne a cikin daya daga cikin dakunan taron majalisar wakilai dake birnin tarayya Abuja.
Shugabannin bankunan sun bayyana goyon bayansu ga mambobin majalisar wakilan game da kira ga a dage ranar daina amfani da tsaffin takardun Naira.
Sun bayyana hakan bayan zamansu da yan majalisar, rahoton ya kara.
Daya daga cikin shugabannin bankunan, Hadiza Ambursa wacce ta wakilci Access Bank ta bayyana cewa abinda ya kamata shine suna karban kudi su zuba cikin na’urorin ATM.
Amma su kansu basu samun isassun kudin.
Hakazalika Shehu Aliyu daga First Bank ya ce ra’ayin yan majalisa na a dage ranar shine maganar gaskiya.