Babu Magoyin Obi da Zai Bar Legas ya Koma Anambra – Reno Omokri
Reno Omokri, tsohon hadimin shugaban kasa kuma daya cikin manyan masu yi wa Atiku Abubakar na PDP kamfen, ya ce babu magoyin Peter Obi, dan takarar LP da zai bar Legas ya koma Anambra.
Omokri ya yi wannan ikirarin ne yayin da ya ke karyata ikirarin cewa Obi, tsohon gwamnan Anambra zai tsamo yan Najeriya daga talauci idan an zabe shi shugaban kasa a zaben da ke tafe.
A cewar Omokri, zai yi yiwuwa a gasgata ikirarin idan da a ce Bola Tinubu na APC ya furta hakan saboda ayyukan da ya yi lokacin yana gwamnan Legas.
Reno Omokri, daya cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, kuma mai goyon bayan dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ya yi wasu maganganu da suka tada kura.
Read Also:
Omokri a shafinsa na Twitter a ranar Laraba da dare ya ce idan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour ya gaza raba al’ummar Anambra da talauci, ta yaya zai iya yin hakan a matakin kasa?
Tsohon hadimin shugaban kasar ya cigaba da cewa idan da a ce Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ne ya furta hakan, da yan Najeriya sun yarda da shi.
Abin da ke faruwa a baya-bayan nan dangane da Bola Tinubu, Peter Obi, Atiku Abubakar, PDP, APC, LP, Zaben 2023
A cewar Omokri, al’ummar Najeriya za su iya ganin nasarorin da Tinubu ya samu lokacin da ya ke gwamnan jihar Legas.
Ya kuma yi tambaya cewa wane cikin magoya bayan Obi, cikin hankalinsa zai bar Legas ya koma Anambra, ya kara da cewa shi kansa Obi a Legas ya ke zaune. Kalamansa:
“Peter Obi bai rage talauci a jihar Anambra ba amma ya yi alkawarin zai rage a kasa. Idan Bola Tinubu ya yi irin wannan alkawarin, za mu iya sauraronsa saboda nasarorin da ya samu a Legas. Wane ‘Obidient’ ne cikin hankalinsa zai bar Legas ya koma Anambra? Ko shi kansa Obi!.”