Ba zai Yiwu na Bar Mulki a Matsayin Wanda ya Gaza ba – Shugaba Buhari
Buhari yace ba zai yiwu ya bar mulki a matsayin wanda ya gaza ba.
Shugaban kasa ya gana da manyan hafsoshin tsaro a ranar Alhamis.
Buhari ya yi farin ciki bisa nasarorin da ake samu kan yan ta’addan Boko Haram.
Abuja – Shugaba Muhammadu Buhari ya lashi takobin cewa ba zai yiwu ya bar mulki a kunyace ba idan ya karashe wa’adinsa na biyu a shekarar 2023.
Ya bayyana hakan yayin zaman majalisar tsaro tare hafsoshin tsaro ranar Alhamis a fadar shugaban kasa dake Abuja, rahoton ChannelsTV.
Mai bada shawara kan lamarin tsaro NSA, Manjo Janar Babagana Munguno, ya mika sakon Buhari ga manema labaran fadar shugaban kasa a karshen ganawar da aka kwashi sa’o’i biyar ana yi.
Read Also:
Yace:
“An yiwa shugaban kasa bayani, kuma ya ji dadi sosai ganin idan dimbin nasarorin da aka samu musamman bayan nadin sabbin hafsoshin tsaro da Sifeto Janar na yan sanda.”
“Kuma ya bayyana cewa bai shirya barin gwamnati a kunyace ba; ba zai yarda hakan ya faru ba.”
An samu nasarar da ba’a taba samu ba Munguno ya kara da cewa abubuwan da suka tattauna akai shine nasarorin da ake samu a faggen yaki a Arewa maso gabas.
Yace:
“Dimbin mutane a Arewa maso gabas dake mika wuya na nuna kokari da jajircewan Sojoji, jami’an leken asiri da sauran jami’an tsaro.”
“Bamu taba ganin irin wannan adadin mutane suna mika wuya ba, hasali hakan na faruwa ne saboda ire-iren abubuwan dake faruwa a faggen dama, lamarin fadace-fadace tsakanin bangarorin yan ta’addan.”