Birai Sun Kwace Jariri ‘Dan Wata ‘Daya Daga Hannun Mahaifiyarsa

‘Yan sanda a Tanzania sun ce wani gungun birai ya mamaye wani gida sannan ya kwace jariri dan wata daya daga hannun mahaifiyarsa.

Biran sun kwace jaririn ne a lokacin da take ba shi nono a wani kauye da ke iyaka da gandun dajin Gombe.

Mazauna kauyen sun yi ta maza sun kwace jaririn daga hannun biran bayan sun yi artabu da su, amma ya mutu daga baya sakamakon raunukan da ya samu a wuyansa da kai.

‘Yan sandan sun ce irin hari na biran ba kasafai ya ke faruwa faruwa ba, sai dai akwai bukatar mutanen da ke zaune a kusa da gandun dajin su rinka kula sosai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here