Ƴan Wasan Barca da za su Buga Wasan Sada Zumunta a Amurka
Hansi Flick ya sanar da ƴan wasa 31 da suka je Amurka, domin shirye-shiryen tunkarar kakar 2024/25.
Barcelona ta sauka a Amurka ranar Litinin tare da Raphinha da Gundo, yayin da sai ranar 1 ga watan Agusta Kounde zai je can.
Ƙungiyar da ta yi fama da ƙalubale a kakar da ta wuce, za ta buga wasan sada zumunta da Manchester City da Real Madrid da kuma AC Milan a Amurka.
Ƴan wasan da Barca ta je Amurka da su
Read Also:
Ter Stegen, Balde, I. Martinez, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña, Christensen, Romeu, Vitor Roque, Gündoğan, Kounde, Julián Araujo, Lenglet, Pablo Torre da kuma M. Casadó.
Sauran sun haɗa da H. Fort, A. Valle, Pau Víctor, Astralaga, Kochen, Unai, Mika Faye, Marc Bernal, Gerard Martín, Noah Darvich, Guille Fernández, Andrés Cuenca, Toni Fernández, Sergi Domínguez, Quim Junyent da kuma Alexis Olmedo.
Ƴan wasan da suke jinya ba a je da su Amurka ba, domin za su ci gaba da zama a Sifaniya.
Barcelona za ta yi atisaye a Amura tun daga Litinin 29 ga watan Yuli zuwa 7 ga watan Agusta.