Shugaba Buhari Ya Nada Sanata Basheer Mohammed a Matsayin Sabon Shugaban Hukumar NAPTIP

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Basheer Mohammed a matsayin sabon shugaban hukumar NAPTIP.

Har ila yau, zasu yi musayar hukuma ne da Imaan Sulaiman Ibrahim wacce ke shugabantar NAPTIP inda zata koma NCFRMI.

Shugaban kasan yace an yi hakan ne domin samun ingancin aiki a karkashin ma’aikatar jin kai da walwalar ‘yan kasa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Basheer Mohammed a matsayin sabon darakta janar na hukumar yaki tare da hana safarar mutane (NAPTIP).

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya sanar da hakan a wata wallafa da yayi a ranar Alhamis a shafinsa na Twitter.

Shehu yace shugaban kasan ya amince da wasu manyan sauye-sauye a ma’aikatar tallafi da jin kai tare da walwalar ‘yan kasa.

Shehu yace an dauka wannan matakin ne domin a samar da burin gwamnati na tabbatar da aiki mai kyau a cikin hukumomin biyu.

Takardar tace Imaan Sulaiman Ibrahim wacce har yanzu take shugaban hukumar NAPTIP za ta mika ragamar hukumar zuwa hannun Basheer Mohammed kwamishinan tarayya na hukumar ‘yan gudun hijira inda ita kuma za ta karba ragamar hukumar da ya baro.

Shehu ya kara da cewa shugaban kasa ya kara bada umarnin sauyin ya fara aiki bayan shirya komai na mika ragamar hukumomin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here