Babu Wanda Yake bi na Bashin Hakuri – Kwamishinan Abia ga ‘Yan Jam’iyyar PDP

Karban bakuncin sanata Orji Kalu da wani kwamishinan Gwamna Ikpeazu yayi na ci gaba da janyo cece-kuce.

Kwamishinan, Cosmos Ndukwe ya karbi bakuncin Kalu wanda ya kasance jigon APC a mahaifarsa da ke Abia.

Sai dai Ndukwe ya bayyana cewa bai aikata kowani laifi ba don ya tarbi jigon na jam’iyyar adawa a jahar.

Guguwar sauyin sheka da tayi wa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tsinke a yankin kudu maso gabas na iya ziyartan jahar Abia kwanan nan yayinda wasu jiga-jigan jam’iyyar suka fara tadi da shugabannin All Progressives Congress (APC) a yankin.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kwamishinan kasuwanni da zuba jari na jahar Abia, Cosmos Ndukwe ya bayyana cewa gwamnan jahar, Okezie Ikpeazu da jam’iyyarsa ta PDP basa binsa bashi don ya karbi bakuncin Sanata Kalu a mahaifarsa.

Legit.ng ta tattaro cewa Ndukwe ya bayyana hakan bayan rigima da cece-kucce da ya barke kan ziyarar da sanatan mai wakiltan Abia ta arewa, Kalu ya kai masa a mahaifarsa ta Akanu Item.

An rahoto cewa kwamishinan yace ziyarar ta ta’aziyya ce sabanin rade-radin cewa ta siyasa ce.

Mataimakin Shugaban karamar hukumar Bande ta jahar, Promise Uzoma Okoro na daga cikin wadanda suka soki kwamishinan.

Ya ce Ndukwe makiri ne tunda ya caccaki kakakin majalisar dokokin Abia, Chinedum Orji kan ziyartan sanatan jam’iyyar mai adawa a baya.

Rahoton ya nuna cewa duk da kiraye-kirayen da ake masa na ba kakakin da sauransu hakuri a kan gagarumin sukar da yayi masa a baya, kwamishinan ya ce babu wanda yake binsa bashi ciki harda gwamnan jahar, Okezie Ikpeazu da jam’iyyarsa ta PDP.

A cewar jaridar, wata majiya kan lamarin ta ce Ndukwe ya bugi kirji a wani taron abokai da yan siyasa a kwanaki cewa babu abunda wani daga cikin wadanda ake magana a kai za su iya yi.

Ya ce babu wanda ke binsa bashin ban hakuri kan abunda yayi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here