Kakakin Majalisar Kasar Amurka ta Nemi a Sauke Donald Trump Daga Kujerar Shugaban Kasa

Kakakin majalisar kasar Amurka, Nancy Pelosi ta yi kira a kan sauke Donald Trump daga kujerarsa.

Nancy ta ce Trump mutum ne mai hatsarin gaske, ya kamata a yi gaggawar tube shi don tseratar da Amurka.

Ta yi wannan kiran ne bayan ta zargi shugaban kasar da cutar da al’umma, zaman shi a kujerarsa akwai matsala.

Kakakin majalisa, Nancy Pelosi, ta bukaci a tube Donald Trump ta hanyar amfani da gyararriyar doka ta 25.

Ta ce wajibi ne a sauke Trump matukar ana so a tseratar da ‘yan kasar da kasar gaba daya. Kamar yadda Pelosi tace, “Tabbas Trump ya ci zarafin mutanenmu da kasar mu.”

Pelosi ta kwatanta Trump a matsayin shu’umin mutum mai mugun hatsari wanda bai dace a bar shi a matsayin shugaban kasa ba, The Nation ta ruwaito.

Sannan shugaban majalisar dattawa, Charles Schumer da safiyar Alhamis ya bukaci a yi amfani da doka ta 25.

Schumer ya ce matsawar ba a yi amfani da dokar ba, za su hada karfi da karfe su tube shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here